Buhari: Ba za mu zuba ido gwamnati ta sake kama Kanu ba – Asari Dokubo

Buhari: Ba za mu zuba ido gwamnati ta sake kama Kanu ba – Asari Dokubo

- Wani tsohon shugaban tsegeru ‘yan Neja Delta ya ce a idon su ba za su yarda a sake kama shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ba

- A cikin wani bidiyo da Asari ya sake ya nuna shakku cewa ba shugaba Muhammadu Buhari ne ya dawo daga Landan ba

- Asari ya zargi kasashen duniya cewa sun yi kunnin doki ga abin da ke faruwa da ‘yan Biyafara

Tsohon shugaban tsegeru ‘yan Neja Delta, Alhaji Mujahid Dokubo Asari, ya bayyana cewa ba za zu yarda gwamnatin tarayyar Najeriya ta sake kama shugaban kungiyar ‘yan asalin yankin Biyafara, IPOB, Nnamdi Kanu ba.

NAIJ.com ta tattaro cewa, Asari, shugaban kungiyar Niger Delta Peoples Salvation Force, NDPSF, ya yi wannan magana ne a cikin wani bidiyo inda kuma ya nuna shakku cewa ba shugaba Muhammadu Buhari ne ya dawo daga Landan ba.

Yayin da yake jawabi da 'yan'uwansa Biyafara ya ce, a yau ba za su zuba ido ko kuma amince da yunkurin gwamnatin tarayya don a sake kama Nnamdi Kanu ba.

Buhari: Ba za mu zuba ido gwamnati ta sake kama Kanu ba – Asari Dokubo

Tsohon shugaban tsegeru ‘yan Neja Delta, Alhaji Mujahid Dokubo Asari

Asari ya ce a cikin bidiyon cewa: “Bayan dawowar abin da suka ce shi ne Muhammadu Buhari, wanda na yi shakka sosai a kai, mutanen da ke kewaye da abin da suka kawo gida daga Landan yana buƙatar kari jini, kuma jinin ‘yan Biyafara ne kai da ni”.

KU KARANTA: Rundunar sojoji Najeriya sunyi Bikin salla tare da yan karkara a garin kareto

"Yaya jini mu zai iya gudana? Hanyar da jinin zai iya gudana ba tare da dadewa ba shine idan aka sake kama Nnamdi Kanu”, a cewar shi.

Ya ce, “Duniya ta nuna kamar ba zu gani abin da ke faruwa ba. Duniya ta yi kunnin doki don jin yadda ake ta kashe ‘yan Biyafara”.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Mahaifin Mikel Obi ya tona asirin yadda dan nasa ya banzatar da shi, ya shekara 5 kenan rabonsu da ko waya

Shekara 5 kenan ko waya bai taba yi min ba - Mahaifin Mikel Obi ya tona asirin yadda dan nasa ya banzatar da shi

Shekara 5 kenan ko waya bai taba yi min ba - Mahaifin Mikel Obi ya tona asirin yadda dan nasa ya banzatar da shi
NAIJ.com
Mailfire view pixel