Abuja: Dalilin da ya majalisar wakilai ta yi watsi da shirin sake kundi tsarin mulkin Najetriya

Abuja: Dalilin da ya majalisar wakilai ta yi watsi da shirin sake kundi tsarin mulkin Najetriya

- Mataimakin shugaban majalisar wakilai ya bayyana dalilin da ya sa majalisar ta yi watsi da shirin sake kudi mulkin Najeriya

- Yusuf ya ce za a sake dawo da batun idan ‘yan majalisa suka dawo daga hutu a watan nan

- Mataimakin ya ce mafi yawan ‘yan majalisa na goyon bayan yunkurin sake fasalin kasar

Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Lasun Yusuf, ya bayyana dalilin da ya majalisar wakilai ta kasar ta yi watsi da shirin sake fasalin kudi tsarin mulkin Najeriya cewa al’ummar kasar ne ba su nuna sha'awa game da batun ba.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Yusuf ya ce majalisar za ta sake dawo da batun in suka dawo daga hutu a watan nan.

Lasun ya fada haka a wata ganawa da 'yan jaridu a Ilobu, garinsa da ke jihar Osun a karshen makon nan.

Abuja: Dalilin da ya majalisar wakilai ta yi watsi da shirin sake kundin tsarin mulkin Najetriya

Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Lasun Yusuf

Ya bayyana cewa mafi yawan ‘yan majalisa na goyon bayan yunkurin sake fasalin kasar, amma suna zargin rashin al’ummar kasar su nuna sha’awa ga al’amarin.

KU KARANTA: Yabon gwani: Babangida ya yaba da salon mulkin shugaba Buhari

Ya yi ikirarin cewa 'yan majalisa wadanda ba su goyi bayan sake fasalin kasar ba, sunyi haka ne saboda mutanen mazabar su ba su amince da hakan ba.

"Amma bishara shine cewa za mu sake dubawa idan muka dawo daga hutu”, inji Yusuf.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel