Abuja: Wani jigon jam’iyyar PDP ya kalubalanci Buhari

Abuja: Wani jigon jam’iyyar PDP ya kalubalanci Buhari

- Tsohon Cif whip na majalisar dattijai ya ce gwamnatin shugaba Buhari ya fi kungiyoyi masu tada kayan baya muni

- Owie ya ce kebe ‘yan kabilar Igbo daga sabon nade-naden da aka yi a kamfanin NNPC alamu nuna kabilanci ne

- Owie ya bukaci shugaba Buhari ya san cewa wannan kasar na dukkanin kabilu ne

Tsohon Cif whip na majalisar dattijai, Roland Owie, ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ya fi wadanda suka ba da sanarwa ficewa daga yankunan su muni.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, Owie ya yi wannan magana ne yayin da yake jawabi kan gyaran bawun kamfanin albarkatun man fetur na kasa, NNPC, wadda ake zargin cewa an ware mutanen yankin kudu maso gabas.

Owie ya ce: “Abin takaici ne ganin yadda muke zargin kungiyar IPOB da matasan arewa da kuma matasan Neja Delta a kan barazanar da zai iya raba kasar, amma jerin mukamai da wannan gwamnati ta yi har zuwa yanzu ya nuna cewa gwamnati ta fi wadanda suka ba ‘yan kabilar Igbo wa’adin ficewa daga jihohin arewa muni”.

Abuja: Wani jigon jam’iyyar PDP ya kalubalanci Buhari

Tsohon Cif whip na majalisar dattijai, Roland Owie

“Mun lura da shirin na yaudara don kebe kudanci, musamman kudu maso gabas a cikin shirye-shiryen wannan gwamnati kuma ana ganin cewa gwamnatin ba ta damu ba, wannan abin bakin ciki ne”, inji Owie.

KU KARANTA: Biyafara : Uwazuruike ya bayyana masu daukar nauyin Nnamdi Kanu dan kawo ma neman yanci kabilan Ibo cikas

"Ina so in yi kira ga shugaba Buhari ya san cewa wannan kasar na dukkanin kabilu ne, bai kamata ya kirkiro wa arewa matsala ba saboda ko yaya yake gani, ba zai iya zama shugaban kasa ba tare da taimakon sauran kabilun kasar ba”, kamar yadda ya shaida wa jaridar Vanguard.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel