Minna: Wani tsohon gwamnan Arewa ya caccaki Andy Uba da Osita Chidoka cewa tuwo yasa suka sauya sheka

Minna: Wani tsohon gwamnan Arewa ya caccaki Andy Uba da Osita Chidoka cewa tuwo yasa suka sauya sheka

- Tsohon gwamnan jihar Nejar, Aliyu Babangida ya zargi wasu ‘yan siyasa cewa abin da za su ci yasa suka canza jam’iyyar

- Babangida ya ce akwai mutanen da suke shiga jam’iyyar kuma suka kasance da ka'idojin ta

- Babbangida ya yi la’akari cewa sauya sheka wani lokaci zai iya kasance matsa lamba daga al'umma

Tsohon gwamnan jihar Nejar, Aliyu Babangida, ya ce wasu mambobi na jam'iyyar adawa ta PDP wadanda suka sauya sheka zuwa wasu jam'iyyu, sunyi hakan ne saboda “abinci" da kuma abin da zai shiga aljihu su.

Musamman tsohon gwamnan na ambaci Andy Uba da Osita Chidoka, yayin da ya ce duk 'yan jam'iyyar PDP masu ruwa da tsaki da suka bar jam’iyyar don wasu dalilai masu inganci za su dawo nan gaba.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, Babangida ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 24 ga watan Satumba a gidansa da ke Minna babban birnin jihar Neja a lokacin ganawa da manema labarai.

Minna: Wani tsohon gwamnan Arewa ya caccaki Andy Uba da Osita Chidoka cewa cin tuwo ya za su sauya sheka

Tsohon gwamnan jihar Nejar, Aliyu Babangida

Tsohon gwamnan ya ce: "A siyasa, akwai mutanen da suke shiga kuma suka kasance da ka'idojin jam’iyyar; akwai kuma wadanda ke shiga don abincin da za su ci; akwai wadanda suke shiga don cimma wasu burin su na siyasa ko kuma wasu dalilai”.

KU KARANTA: Zan cigaba da yin bakin kokari na Inji Shugaban kasa Buhari

Saboda haka, sauya sheka wani lokaci ba zai iya zama dalili guda daya ba, wani lokaci ma zai iya kasance matsa lamba daga al'umma.

A kwanan nan, Andy Uba da Osita Chidoka, manyan 'yan jam'iyyar PDP masu karfin gaskiya sun koma jam’iyyar mai mulki ta APC da kuma jam’iyyar ta United Progressives Party bi da bi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel