Buhari ba shi da masaniya cewa hanyar jirgin kasa zai wuce ta garinsa Daura – inji ministan sufuri

Buhari ba shi da masaniya cewa hanyar jirgin kasa zai wuce ta garinsa Daura – inji ministan sufuri

- Ministan sufuri ya ce shugaba Buhari bai san cewa hanyar jirgin kasa zai wuce ta Daura ba

- Amaechi ya ce shugaban Buhari ya bukaci a hade jihohin Kebbi da Zamfara da kuma Sakkwato ta hanyar jirgin kasa

- Minstan ya ce shugaba Buhari ya umarni su hade dukkan biranan jihohi ta 36 ta hanyar jirgin kasa

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi ikirarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai san cewa hanyar jirgin kasa zai wuce ta garinsa Daura ba wanda ke jihar Katsina.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, ministan ya kara da cewa shugaban ya bukaci a hade jihohin Kebbi da Zamfara da kuma Sakkwato ta hanyar jirgin kasa.

Ya ce: "Shugaban ya kira kaina da ministan mukamashi, ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, cewa mu ci gaba da ayyuka na gina kasar kuma ya fada mini musamman cewa dole ne in hade dukkan biranan jihohi ta 36 ta hanyar jirgin kasa. Wannan babban aiki ne”.

Buhari ba shi da masaniya cewa hanyar jirgin kasa zai wuce ta garinsa Daura ba – inji ministan sufuri

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi

“Bisa umarnin shugaban kasa, yanzu haka muna tsara layin hanyar jirgin kasa wanda zai hada Gusau, Sakkwato da kuma Kebbi”, inji shi.

KU KARANTA: Buhari ya sake nuna muna kabilanci – Inji Ohaneze Indigbo

“Shugaban kasa bai san cewa hanyar jirgin kasa zai wuce ta Daura ba. Lokacin da na gan shi a kan kafofin watsa labarun cewa shugaban ya amince da aikin jirgin kasa zuwa garinsa abin da Jonathan bai taba yi ba, sai na yi mamaki domin wannan ba gaskiya bane”.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel