Biyafara : Uwazuruike ya bayyana masu daukar nauyin Nnamdi Kanu dan kawo ma neman yanci kabilan Ibo cikas

Biyafara : Uwazuruike ya bayyana masu daukar nauyin Nnamdi Kanu dan kawo ma neman yanci kabilan Ibo cikas

- Belin da aka ba wa Kanu yaudara ce kawai

- Jami'an tsaro sun tunkari Nnamdi Kanu ne bayan sun ji shi yana kururuwa a Radiyo

- Ralph Uwazuruike ya zargi gwamnatin jam’iyyar All Progressive Congress da daukan nauyin Kanu

Wanda ya kafa kungiyan neman yancin yan asalin Biyafara, IPOB, Ralph Uwazuruike, ya zargi gwamnatin jam’iyyar All Progressive Congress, APC da ba shugaban IPOB Nnamdi Kanu makudan kudaden dan kawo ma fafitukar da suke yi cikas.

Uwazuruike yayi wannan furucin ne a lokacin da yake zantawa da yan jarida.Ya ce kokarin da yake yi na samar da Biyafara, “ta hanyar zaman lafiya” ya samu tangarda ta dalilin Kanu wanda “jami’an tsaro suke amfani dashi wajen kawo karshen gwagwarmayar su.

Wanda ya kafa kungiyan MASSOB yace shugaban IPOB ya zo ne dan ya rusa gwagwarmayar su na samar da Biyafara, kuma zai fara ne ta hanyan hana zaben Anamabara da za’ayi 18 ga watan Satumba, wanda yace kada kowa ya fito kada zabe.

Biyafara : Uwazuruike ya bayyana masu daukar nauyin Nnamdi Kanu dan kawo ma neman yanci kabilan Ibo cikas

Biyafara : Uwazuruike ya bayyana masu daukar nauyin Nnamdi Kanu dan kawo ma neman yanci kabilan Ibo cikas

Ya ce Belin da aka bashi “yaudara ce kawai,” Uwazuruike yana mamakin cewa tun da aka sako Kanu bayan ambashi beli sabdoda rashin lafiya bai ziyarci kowani asibiti ba.”

KU KARANTA : An kama wani Shahararren mai garkuwa da mutane a Enugu

Ya kara da cewa,“Nnamdi Kanu yana yaki da yan Biyafar ne kawai. Kuma jami’an tsaro suna amfani da shi.

Sun tunkare shi ne bayan "Sun ji shi yana kururuwa a radiyon Biyafara kuma ya amince da yin aiki da su.”

“Babu zabe a jihar Anambara, yunkurin ne na jam’iyyar APC wajen kawo karshen gwamnatin Obiano ta hanyan kawo rudani a jihar" wannan shine abun dake faruwa, kuma jami’an tsaro ne suka hada wannan wajen amfani da Kanu.

“Nasan manyan gidajen da Nnamdi Kanu da ire-iren sa suke da shi a kasashenn waje. Kanu ya cigaba da kunyatar da kanshi Kaman yadda yake yi yanzu , saboda wasu daukan nauyin sa, kuma nasan masu daukan nauyin sa.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel