Yabon gwani: Babangida ya yaba da salon mulkin shugaba Buhari

Yabon gwani: Babangida ya yaba da salon mulkin shugaba Buhari

Hakika abunda shugaba Buhari yayi na gayyatar shugabannin jam'iyya adawa ta PDP tare da jam'iyya mai mulki ta APC a kwanan baya lokacin da ya gana da su duka a babban dakin taro na fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja a cewar tsohon Gwamnan jihar Neja Dakta Mu'azu Babangida Aliyu.

Dakta Mu'azu din dai yayi wannan kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugannin kungiyar yan jarida ta jihar Neja a gidan sa dake a Minna babban birnin jihar a karshen satin nan da ya gabata.

Yabon gwani: Babangida ya yaba da salon mulkin shugaba Buhari

Yabon gwani: Babangida ya yaba da salon mulkin shugaba Buhari

KU KARANTA: Yadda shiga harkar fim ta maida ni mutunniyar kirka - Jaruma

NAIJ.com ta samu daga majiyoyin mu cewa Dakta Babangida ya kuma ce wannan abun da shugaba Buhari din yayi ya taimaka sosai wajen kawo wa kasar nan zaman lafiya musamman ma dai a tsakanin magoya bayan jam'iyyun biyu.

Haka ma dai tsohon Gwamnan jihar ta Neja ya ba shugabannin jam'iyyar ta PDP shawarar cewa yanzu lokaci ne da za su tsaya su gyara jam'iyya domin su tunkari zabuka masu zuwa.

Daga karshe kuma sai ya nuna jin dadin sa game da hukuncin da babbar kotun kasar ta yanke da ya kawo karshen takaddamar mulkin jam'iyyar tasu a kwanan baya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel