Lokacin fatattakar masu yi maka kafar angulu fa yayi - Shehu Sani ya fadawa Buhari

Lokacin fatattakar masu yi maka kafar angulu fa yayi - Shehu Sani ya fadawa Buhari

Sanata mai wakiltar jama'ar yankin jihar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai Sanata Shehu Sani yayi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya gaggauta fatattakar masu yi masa kafar angulu a cikin gwamnatin sa domin samun cigaba mai anfani.

Sanatan yayi wannan kiran ne a garin sa na Kaduna yayin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala shagulgulan sallah. Sanatan ya bayyana cewar yin hakan ne kawai zai tabbatar wa da talakan Najeriya cewa shugaba Buhari din yana kaunar sa.

Lokacin fatattakar masu yi maka kafar angulu fa yayi - Shehu Sani ya fadawa Buhari

Lokacin fatattakar masu yi maka kafar angulu fa yayi - Shehu Sani ya fadawa Buhari

KU KARANTA: Da Abacha yayi tsawon rai da Najeriya ta wuce haka

NAIJ.com ta samu dai cewa Sanatan ya ba Buhari shawarar yayi karatun ta-nutsu sannan ya duba dukkan wadanda ya zuwa yanzu ba sa tsinana komai a gwamnatin ta sa sannan ya kore su ya kuma maye gurbin su da wasu sabbi.

Sanatan ya kuma kara da cewa yanzu dai gwamnatin ta shugaba Buhari tayi shekatu biyu da yan watanni kuma dole ne a samu wasu daga cikin ministocin sa a gajiye don haka akwai bukatar kawo sabbin jini domin su cigaba daga inda suka tsaya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel