Buhari ba ya Najeriya - Nnamdi Kanu

Buhari ba ya Najeriya - Nnamdi Kanu

- Shugaban IPOB ya bayar da tabbacin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ya Najeriya

- Ya kuma yi tir da gidan jaridar THE SUN bisa wallafar labaru na karya akan sa

- Ya yi kira ga magoya bayansa wajen yin watsi da duk wani abu da suka ji daga kafofin watsa labarai

Sahara reporters ta ruwaito cewa, shugaban 'yan asalin yankin Biyafara, Nnamdi Kanu, ya bayar da tabbacin cewa, wanda yake mulkar Najeriya a yanzu haka ba shugaba Buhari ba ne, domin kuwa gwamnatin Najeriya ta dauka hayar wani ne mai kira da kuma zubi irin na Buhari wajen ci gaba da mulkar kasar nan.

A kalamansa, "Mutumin da kuke kallo a gidajen talabijin ba Buhari ba ne, daga kasar Sudan yake. Bayan aiki na tiyata da kwararrun likitoci suka gudanar shine aka kawo shi kasar nan. An koya wa mutumin halayya da kuma dabi'u irin na Buhari saboda haka kar ya rude ku. Zan iya tsayawa kuma in tabbatar da ko ni waye, amma Buhari ba zai iya yin haka ba, domin haka ba zai iya yaudarar Nnamdi Kanu da IPOB ba," in ji shugaban IPOB.

Buhari ba ya Najeriya - Nnamdi Kanu

Buhari ba ya Najeriya - Nnamdi Kanu

Kanu ya bayyana cewa, babban kuskuren da Buhari ya yi a baya shine, daurin da sanya aka yi masa, sanadiyar bayyana ra'ayin shi da kuma shugabancin 'yan asalin yankin Biyafara a kan fafutukar neman yankin su.

KU KARANTA: Zan kashe duk wanda ya taɓa matata – Inji wani babban Fasto

Shugaban na IPOB ya yi tir da kamfanin jaridar THE SUN, bisa wallafa labarun karya da suka shafe shi, da cewar wai ya arce.

Ya kara da cewa, ba shi da ra'ayin yin wani furuci, amma yanzu ya zamto tilasa ne a agare shi sanadiyar karairayi da gidajen jaridu suka wallafawa akansa don kawai jaridar su ta samu shiga a kasuwa.

Ya kuma shawarci magoya bayansa akan yin watsi da duk wani abu da suka gani ko kuma suka saurara daga kafofn watsa labarai, face abin ya zo daga gare shi ne.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel