Rikita-rikita: Patience Jonathan ta tari aradu da ka, ta kwace Otel din ta da EFCC ta kwace

Rikita-rikita: Patience Jonathan ta tari aradu da ka, ta kwace Otel din ta da EFCC ta kwace

Da alama dai wani babban rikici na neman ballewa tsakanin hukumar nan dake yaki da masu yi ma tattalin arzikin kasa ta'anadi watau EFCC da kuma uwar gidan tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan bayan da ta kwace wani otel din ta da aka kama.

Majiyar mu dai da ta binciko yadda lamarin yake ta gano cewar Patience Jonathan ta goge rubutun da hukumar ta EFCC tayi a otel din nata inda kuma tuni ta fara anfani da shi tun bayan da hukumar ta rufe mata shi.

Rikita-rikita: Patience Jonathan ta tari aradu da ka, ta kwace Otel din ta da EFCC ta kwace

Rikita-rikita: Patience Jonathan ta tari aradu da ka, ta kwace Otel din ta da EFCC ta kwace

KU KARANTA: Fastocin Abdulaziz Yari sun malale titunan Katsina

NAIJ.com ta kuma tabbatar daga majiyar mu cewa da aka tambayi masu gadin gidan ko ya akayi suka shigo gidan sai suka ce uwar gidan su ce ta umurce su da yin hakan yayin da kuma suka bukaci dukkan mai tambaya ya je wurin ta.

Haka zalika da majiyar mu ta tambayi mai magana da yawun hukumar ta EFCC Mista Wilson Uwujaren game da lamarin sai ya kada baki yace shi ma bai san da maganar ba don haka kuma ba zai iya yin tsokaci game da lamarin ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel