Abin da matar Adeboye ta ce game da lafiyar Buhari

Abin da matar Adeboye ta ce game da lafiyar Buhari

- Matar Adeboye ta jagoranci dimbin mabiya cocin RCCG wajen hidimar Ruhi mai tsarki

- Mun gode wa Allah da ya dawo da shugabankasar Najeriya cikin koshi lafiya

- Muna rokon Allah da yayi mana magannin azzaluman Najeriya

Folu, matar shugaban cocin Redeemed Christian church of God, RCCG, Fasto Enoch Adebayor ta roki Allah da ya kammala warkar da shugabankasa Muhammadu Buhari.

Matar Adeboye wace ta jagoranci dumbin mabiyan cocin wajen taron ‘Hidimar Ruhu Mai Tsarki’ sun mika godiya ga Allah da yasa shugaban kasa ya dawo cikin koshin lafiya.

"Mun yi addu'a ga Allah da ya warkar da shi daga duk wani nau'i n rashin lafiya, kuma Allah ya amsa addu'o'inmu kuma ya dawo mana dashi cikin koshin lafiya, amma muna rokon Allah ya kammala warkar da shi don cika aikin da ya turo sa na mulkin kasar nan," Inji ta a lokacin da ta jagorancin taron yin addu'o’i.

Ta kuma gode wa Allah da ya yi amfani da Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo wajen rike kasar a lokcin da shugabankasa ke jinya a kasar Birtaniya.

Abin da Adeboye yace game da lafiyar Buhari

Abin da Adeboye yace game da lafiyar Buhari

KU KARANTA:Bikin Idi: An yi hawa saboda murnar samun lafiyar Shugaba Buhari a Daura

Ta ci gaba da yin addu'a, da cewa: "Allah yayi maganin dukan masu zaluntar mu a Najeriya, ya wadatatar da al’ummar Najeriya da arziki mai amfani, kuma ya kiyyaye shugabanin mu daga sharrin makiyan su."

“Muna su mu fita daga cikin wahala."

A lokacin da Babban Fasto Enoch Adeboye yake jawabi na musamman ga mahalarta ‘Hidimar Ruhi Mai Tsarki’ don amfanin 'ya'yan Ubangiji,wanda aka gudanar a New Arena, ya kara tunatar da mabiyan sa akan wahayin wannan shekarar da aka sanar da shi game da cigaban da Najeriya za ta samu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Abubakar Shekau yayi sabon bidiyo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel