Binciken EFCC ya kara nusantawa akan gidajen Diezani na Dubai

Binciken EFCC ya kara nusantawa akan gidajen Diezani na Dubai

Bayan kusan makonni biyu da sanya hannu cikin yarjejeniyar gwamnatin Najeriya da na nahiyyar hadin kan kasar larabawa, gwamnatin Najeriya ta shirya kwace kadarorin tsohuwar ministan ma'adanan man fetur, Mrs Diezani Alison Madueke da wasu 'yan kasar nan guda uku.

Sauran mutanen da EFCC ta shiga takun saka da su sun hadar da; tsohuwar shuganban bankin Oceanic, Misis Cecilia Ibru da tsohon ministan birnin tarayya Sanata Bala Mohammed tare da dan sa Shamsudeen.

Hukumar EFCC ta binciko wasu gidaje guda takwas da ake zargin na Cecilia ne da kuma wasu gidajen biyu na tsohon minista Bala, inda a yanzu haka akwai jerin sunayen mutane 25 'yan kasar Najeriya da ake zargin su da mallakar kadarori a birnin Dubai ta hanyar saye da kudin da suka wawushe na Najeriya.

Sakamakon gudanar da bincike na hukumar EFCC, an gano cewar Diezani ta na da wasu gidaje na alfarma wanda jimillar kudin su ya tashi kusan dirhami miliyan 77.

Binciken EFCC ya kara nusantawa akan gidajen Diezani na Dubai

Binciken EFCC ya kara nusantawa akan gidajen Diezani na Dubai

Jaridar THE NATION ta buga a shafin ta na ranar lahadin da ta gabata cewa, wasu daga cikin abokan kasuwancin Diezani ne suka baiwa hukumar EFCC tallafi wajen gudanar da binciken ta.

KU KARANTA: Zan kashe duk wanda ya taɓa matata – Inji wani babban Fasto

A kwana-kwanan nan, gwamnatin Najeriya za tayi umarni ga gwamnatin Dubai domin karbe wannan gidaje na tsohuwar ministan bisa ga wata yarjejeniya da suka kulla da shugaban kasa Muhammadu buhari tun a ranar 19 ga watan Janairu na shekarar da ta gabata.

Wannan yarjejeniya ta kunshi bayar da duk wani taimako wajen kamawa da kuma gurfanar da duk wani dan kasar Najeriya da bincike ya nuna ko kuma ake zargin sa da aikata wani laifi da ya danganci keta dokokin Najeriya.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel