Idan Gwamnanti tayi wasa Najeriya za ta rabe - C.A.N

Idan Gwamnanti tayi wasa Najeriya za ta rabe - C.A.N

- Kungiyar CAN tace idan Gwamnanti tayi wasa Najeriya za ta rabe

- CAN ta taya Musulman Najeriya murnar sallar idi a fadin kasar

- Shugaban Kungiyar yayi gargadi yace wani yaki na iya barkewa

Kungiyar Kiristocin kasar nan watau CAN tace Najeriya za ta tarwatse idan aka yi sake a halin yanzu.

Idan Gwamnanti tayi wasa Najeriya za ta rabe - C.A.N

Kungiyar C.A.N ta gargadi Gwamnati

Shugaban Kungiyar CAN na kasa Samson Ayokunle yayi gargadi yace wani yaki na iya barkewa a Najeriya idan Gwamnatocin Jihohi da Tarayya ba su dage wajen kawo karshen rabe-raben da ke Kasar ba. Shugaban CAN yace babu kasar da ta fita lafiya bayan yake-yake sau biyu.

KU KARANTA: An kai hari ga 'Yan Boko Haram yayin bikin idi

Samson Ayokunle ya taya Musulman kasar murnar bikin Sallah ya kuma kira su da su yi riko da littafin Al-kurani da kuma zama na gari a ko yaushe. Ayokunle ya kuma kira masu rike da mulki su cika alkawarin da su dauka lokacin neman zabe.

Tsohon Shugaban Jami’ar A.B.U Zariya Farfesa Ango Abdullahi yace ana bukatar samun shugabannin da za su iya rike arzikin da Najeriya ke da shi. A cewar sa hakan ba wai raba kasar ko arziki bane zai kawo ga ci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

A same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Fatawar Malaman Musulunci game da layya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel