An damke wasu 'Yan Boko Haram a Kano - Gwamna Ganduje

An damke wasu 'Yan Boko Haram a Kano - Gwamna Ganduje

– Ashe ‘Yan Boko Haram sun yi kokarin kai hari a Kano

– Gwamnan Jihar Kano Dr. Ganduje ya bayyana wannan

– Ganduje ya bayyana hakan ne wajen Hawan Nasarawa

Mun ji cewa ashe 'Yan Boko Haram sun yi yunkurin kai hari a Kano lokacin Bikin Sallar nan daga Jaridar Daily Trust.

An damke wasu 'Yan Boko Haram a Kano - Gwamna Ganduje

Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Ganduje

Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa an kama wasu 'Yan ta'addan Boko Haram da dama a Jihar Kano kwanan nan daf da lokacin Sallah. Gwamnan yace 'yan ta'addan sun yi niyyar kai hare-hare ne a fadin Jihar.

KU KARANTA: Makamai sun yi kafafu a Najeriya

Gwamna Ganduje ya yabawa kokarin Gwamnatin Buhari wajen yaki da ta'addanci kuma yace Jihar Kano ta bi sahu. Ganduje ya bayyana irin kokarin da Jami'an tsaro su kayi wajen ganin bayan 'yan ta'addan a wajen bikin hawan Nasarawa jiya.

Kamar yadda mu ka samu labari 'Yan ta'addan Boko Haram sun ji ba dadi lokacin Bikin babban Sallar nan. Sojojin saman Najeriya ne dai su ka yi masu wani luguden wuta a Dajin Sambisa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta bayyana ashe mashawartan Buhari sun gaya masa wanda ya kamata ya zama shugaban NIA, amma yayi watsi da shawaras

NAIJ.com
Mailfire view pixel