Boko Haram: 'Yan ta'adda sun ji ba dadi lokacin Bikin Sallah

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun ji ba dadi lokacin Bikin Sallah

- 'Yan Boko Haram sun gamu da hare-hare a lokacin Bikin Sallah

- Sojojin saman Najeriya ne dai su ka yi masu wani luguden wuta

- Har yanzu akwai wasu 'yan ta'addan Boko Haram a Dajin Sambisa

Kamar yadda mu ka samu labari 'Yan ta'addan Boko Haram sun ji ba dadi lokacin Bikin babban Sallar nan.

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun ji ba dadi lokacin Bikin Sallah

Sojojin sama sun tarwatsa 'Yan Boko Haram

Rundunar Sojojin saman Najeriya sun yi wa 'Yan Boko Haram wani luguden wuta lokacin da su ke bikin Idi a cikin Dajin Sambisa. Sojojin saman kasar sun harbawa 'Yan ta'addan bama-bamai bayan harin sama da jiragen F7-Ni, Alpha Jet da kuma L-39 ZA.

KU KARANTA: Makaman 'Yan sanda sun shiga rububi

Wani mai magana da bakin Sojojin saman kasar kwanaki ya bayyana yadda su ka budawa 'Yan Boko Haram din wuta a Garin Maloma bayan a Dajin Sambisa sun hange cincirindon 'Yan ta'addar karkashin wata bishiya.

Idan ba ku manta ba Laftana-Janar Tukur Yusuf Buratai ya bada kwanaki 40 a damke Shugaban wani bangaren Kungiyar 'Yan ta'addan Boko Haram Abubakar Shekau. Sai ga shi wannan wa'adi ya kare amma shiru.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shugaban Boko Haram ya maidawa Buratai martani

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel