Yajin aiki: Gwamnati za ta zauna da ASUU idan an dawo hutu

Yajin aiki: Gwamnati za ta zauna da ASUU idan an dawo hutu

- Gwamnati ta bayyana lokacin cigaba da ganawa sa ASUU

- Da zarar an gama hutun bikin babban Sallah za a shiga zama

- Ministan kwadago na kasar Dr. Chris Ngige ya bayanna haka

Ministan kwadago Chris Ngige ya bayyana cewa za a cigaba da zama da ASUU bayan bikin Sallah.

Yajin aiki: Gwamnati za ta zauna da ASUU idan an dawo hutu

Ministan kwadago Chris Ngige

Gwamnatin Tarayya za ta cigaba da zama da Kungiyar ASUU ta Malaman Jami'a da zarar an dawo hutun Sallah a Kasar. Ma'aikatar kwadagon kasar ya sanar sa wannan ta bakin wani Mataimakin Darektan ta Samuel Olowookere.

KU KARANTA: An yi wa Shugaba Buhari hawa a Daura

Yajin aiki: Gwamnati za ta zauna da ASUU idan an dawo hutu

Kungiyar ASUU na Malaman Jami'a

Ma'aikatar kwadagon na taimakawa Ma'aikatar ilmi wajen kawo karshen yajin aikin da Malaman Makarantar su ka shiga kwanakin baya. Ba dai yau Kungiyar ASUU su ka fara shiga yajin aikin ba wanda Ministan yace yana sa ran kawo karshen lamarin kwanan nan.

Mun fahimci cewa wasu Jama'a sun koka game da shirun Shugaban kasa Buhari game da yajin aikin ASUU. Har yanzu Shugaban kasar da kan sa bai ce komai ba ga Malaman Jami’ar ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

'Yan wasan Najeriya sun lallasa Kamaru

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel