Buhari ya sake nuna muna kabilanci – Inji Ohaneze Indigbo

Buhari ya sake nuna muna kabilanci – Inji Ohaneze Indigbo

- Kungiyar ‘yan kabilar Igbo ta koka kan sabon naddin da aka yi a kamfanin NNPC

- Kungiyar ta zargi shugaba muhammadu Buhari da nuna kabilanci

- Ohaneze ta ce irin wannan al’amari ya sa matasa a yankin ke fafutukar ballewa daga Najeriya

Kungiyar ‘yan kabilar Igbo, Ohaneze Ndigbo, ta sake zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da nuna kabilanci a cikin ayyukansa.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, kungiyar ta zargi shugaba Buhari da nuna wa ‘yan kabilar Igbo banbanci a wata gyaranbawu da aka yi na kwanan nan a kamfanin albarkatun man fetur ta kasa, NNPC, inda ta ce an yi watsi da kudu maso gabashin kasar.

A cewar Ohanaeze, irin wannan al’amari ya sa matasa a yankin ke fafutukar ballewa daga Najeriya.

Buhari ya sake nuna muna kabilanci – Inji Ohaneze Indigbo

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Matsayin Ohaneze ya kasance wani ɓangare na wata sanarwa da shugaban kungiyar, John Nwodo ya sanya hannu a Abuja ranar Lahadi, 3 ga watan Satumba.

KU KARANTA: Tuna baya: Buhari ya hadu da 'Yan ajin su na Sakandare a Daura

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta bayyana karara a cikin sabon nade-naden manajoji na kamfanin NNPC inda shugaban ya fifita Arewa, yayin da kuma ya yi watsi da kudu maso gabas da gangan, kamar yadda ya kasance tun lokacin da ya karbi mulki a shekarar 2015.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel