Aikin Hajji: Innalillahi Wa’inna Ilaihirraji’un (Hotuna)

Aikin Hajji: Innalillahi Wa’inna Ilaihirraji’un (Hotuna)

- Allah ya yiwa wata matashiya rasuwa a hanyar ta Mekkah a lokacin gudanar da aikin hajji

- Ana bukatar idan akwai wanda ya san ta a sanar da iyalinta

- Yawan mahajjata na Najeriya wadanda suka mutu a aikin hajjin na yanzu ya karu daga 5 zuwa 7

An kaddamar da sanarwa a yanar gizo don gano dangi wannan matashiyar wanda ta samu cikawa a hanyar ta zuwa Makkah a Saudi Arabia lokacin gudanar da aikin hajji. Wani mutun mai suna Mumuni Iddisah wanda yake aikin hajji a ƙasa mai tsarki, ya raba hoto na marigayiyar kuma ya rubuta;

“Wannan matashiyar Allah ya mata cikawa a Mekkah a lokacin gudanar da aikin hajji, idan akwai wanda Allah yasa ya san ta a sanar da iyalinta. Don Allah a yi kokarin raba wannan hoton don mu iya gano iyalinta. Na gode”.

Idan de baku manta ba NAIJ.com ta ruwaito cewa yawan mahajjata na Najeriya wadanda suka mutu a aikin Hajjin na yanzu ya karu daga 5 zuwa 7 kamar yadda jami'ai suka bayyana.

Aikin Hajji: Innalillahi Wa’inna Ilaihirraji’un (Hotuna)

Wasu mahajjatan Najeriya a kasar mai tsarki, Mekkah

KU KARANTA: Babbar Sallah a Jihar Borno: Labari cikin Hotuna

Shugaban hukumar aikin hajji na Najeriya, NAHCON, Abdullahi Mohammed, ya bayyana hakan a wata hira da 'yan jarida a Mount Arafat da ke Saudi Arabia a ranar Alhamis da ta gabata.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel