Kaicho! Wata Amarya 'yar shekaru 17 ta kashe jinjirin kishiyar ta da guba

Kaicho! Wata Amarya 'yar shekaru 17 ta kashe jinjirin kishiyar ta da guba

-Zafin kishi yasa wata mata yar shekara 17 ta shayar da jaririn kishiyar ta guba

-A cewarta auren dole akayi mata kuma mijin nasu daga baya ya juya mata baya

-Hindatu dai tayi ikirarin yin nadama a duk lokacin da ta tuna da wannan danyen aiki

Wata mata 'yar shekaru 17 ta bayyana cewar kiyayyar da take wa mijinta ya sa ta shayar dan sa guba wanda mahaifiyar sa kishiyarta ce. Ita dai Hindatu 'yar Jihar bauchi ce a kauyen Wuro Bogga a garin Duguri dake karamar hukumar Alkaleri. Ta auri mijin nata mai suna ori Abdullahi shekaru 2 da suka wuje bisa tilastawan mahaifinta.

Kaicho! Wata mata ta kashe dan kishiyar ta da guba
Kaicho! Wata mata ta kashe dan kishiyar ta da guba

Hindatu ta bayyana ma manema labarai a hedkwatan 'yan sanda na Jihar bauchi yadda ta auri mijinta a matsayin matarsa ta biyu ba a son ranta ba sai don bin umurnin iyayenta. Ta bayyana yadda suke zaman doya da manja tsakaninta da mijin ta da kishiyarta. Daga bisani dai mijin nata yana son ta amma kwatsam sai ya fara gallaza mata yana cutar da ita. Iyayenta basu yarda da maganarta ba ko da ta kai masu koke, a cewar ta.

DUBA WANNAN: Kishin-kishin: Dangote ne dan takarar a PDP 2019

Hindatu dai ta tabka wannan danyen aiki ne Alhali mijin nata yana saudiyya don aikin hajji ita kuna kishiyar nata bata gida. A cewar ta, ta dauki jinjirin kishiyar nata dan wata biyu ta kai shi dakinta a inda tayi kokarin sharyar da shi guban sai ya ki sha. Nan take ta yi farga da munin aikin da tayi niyya tayi maza ta cire rigar sa ta share masa gubar da rigar.

Hindatu dai tayi ikirarin yin nadama a duk lokacin da ta tuna da wannan danyen aiki. Ta kuma ce a shirye take da fuskanci duk wani hukunci da za'a zartar a kanta. Ta kuma kara da cewan Mijin nata da aka kira shi ta waya yayi alwashin sakin ta da zaran ya dawo daga aikin hajji.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel