Bayan shekaru 38 da haka kabarinsa - wani mutum ya ce ga garinku nan

Bayan shekaru 38 da haka kabarinsa - wani mutum ya ce ga garinku nan

Shafin Legit.ng ya kawo muku labarin wani mutumin da ya shirya wa jana'izarsa ta hanyar haka kabarinsa da bayyana wasiyarsa shekaru 38 a baya kafin muturwarsa a yanzu.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan mutum mai sunan Stanley Muriuki Njuki, ya shiryawa mutursa shekaru 38 baya kafin mutuwar ta cin ma sa a yanzu, wanda ya haka kabarin sa tun a shekarar 1979.

Muriuki wanda mazaunin kauyen Karogoto ne, na garin Nyeri dake kasar Kenya, ya bayar da wasiyar irin kayan tufafi da kuma kalar katakon akwatin daukar gawa da ya ke so a sanya shi kuma a binne shi a ciki.

Marigayi muriuki wanda sanannen lauya ne a kasar a yayin rayuwarsa, ya gina wani daki da yake son iyalan sa su sanya shi na tsawon kwanaki takwas kafin su binne shi a kabarin sa.

Bayan shekaru 38 da haka kabarinsa - wani mutum ya ce ga garinku nan
Bayan shekaru 38 da haka kabarinsa - wani mutum ya ce ga garinku nan

Ya bayar da wasiyar sanya gawar ta sa akan gawayi da kashin kafinta da kuma wasu nau'ukan tsirai da ya sanya a cikin dakin.

Ya kuma bayar da wasiya ga 'ya'yansa akan duk bayan wani lokaci su zuba wa gawar ta sa ruwan sanyi kuma su yi gadin gawar saboda kar beraye su kusance ta.

KU KARANTA: Yanzu Yanzu: Allah yayi ma tsohon Sanata Kanti Bello rasuwa

Daya daga cikin 'ya'yan sa, Charles, ya bayyana cewa, "A lokacin da yake karami bai san dalilin mahaifin na su na haka kabarainsa ba, sai bayan ya girma ya fuskanci muhimmancin wannan abu da mahifin ya yi kuma ya sanya shi cikin jiga-jigan rayuwar mu."

Ya bar min wasiyar cewa, an tsare gawar sa na tsawon kwanakin da zai yi don kar beraye su gutsuri kunne ko hancin sa a yayin da ya ke mace."

Charles ya ce, "ba su da halin binne shi cikin irin akwatin da ya umarta sanadiyar tsardar sa, sai dai sun samo icen wannan bishiya da yake so a binne shi a cikin akwatin da aka kera daga ita, inda suka shinfida wannan katako a gefen wannan akwatin na sa."

A cewar Charles, "mun yi iyaka bakin kokarin mu wajen bin umarnin wasiyar mahaifin mu, kuma akwai wasiyar da ya bari na cewa, kar a kai shi asibiti idan cuta ko rashin lafiya ta kama shi sannan bai bukatar wani likita ya duba shi."

KU KARANTA: Ko a tarihi ba a taba samun gwamna kamar Wike ba - APC

Makwabta suma sun bayyana Muriuki da cewar mutum ne mai tsaurin ra'ayi da kafuwa akan abu, inda wani ya ce: "Na tuna kimanin shekaru takwas da suka gabata, wani dan babur ya buge shi, kuma muka yi kokarin gaggauta shi zuwa asibiti amma ya bukaci a dawo da shi gidansa, yana cewa shi ba bu abin ya same. Ba mu da wani zabi face dawo da shi gida duk da raunukan da ya samu."

Wani makwabcin na sa kuma, Johnson Thairu, ya bayyana cewa, " Na taba tambayarsa dalilin da yasa ya haka kabarin sa tun kafin mutuwarsa, ya kuma ce min yana da matukar mahimmanci idan ba a damu da abin da iyalan sa za su kashe wajen binne shi ba."

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, hukumar lafiya ta kasar, ta umarci iyalan na sa da ko su binne wannan gawa ko kuma su mika ta mutuwari, inda aka bar su ba bu zabi face suka binne shi bayan kwana guda da mutuwar sa.

Daga wata majiya kuma, marigayi Muriuki ya shaidawa 'yan jarida a shekarar 2012 cewa, yana son a binne shi kamar yadda aka binne duk wani Fir'auna na kasar Masar da suka gabata.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel