Gobara: Wuta ta lashe dakunan daliban jami’ar Filato

Gobara: Wuta ta lashe dakunan daliban jami’ar Filato

- Gobara ta tashi a dakunan kwanan dalibai na jamiár Filato

- Ta lashe komai na dakunan kafin ta mutu

- Ba'a rasa rai ko guda ba

Rahotanni sun kawo cewa gobarab ya tashi a sahin kwanan dalibai na Jami’ar fasaha dake jihar Filato da misalin karfe 8:30 na safiyar ranar Litinin, 28 ga watan Agusta inda dingi ci har karfw 11:44.

Tuni dai wasu dalibai suka ci na kare a yayinda gobarar ta fara ci inda wasu suka nuna jarumta ta hanyar tsayawa su kasha wutar sai dai basu samu nasaran aikata hakan ba.

Yusuf Ade da ke aikin gadi a makarantan ya ce daliban sun tafi aji a lokacin da gobarar ta fara amma ko tsinke ba a ciro ba daga dakunan daliban.

Gobara: Wuta ta lashe dakunan daliban jami’ar Filato

Gobara: Wuta ta lashe dakunan daliban jami’ar Filato

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ta ce hukumar kashe gobara ta jihar ta iso wajen wutar ne bayan gobarar ta cinye komai dake dakunan.

Wani jami’in makaranta Dauda Gyemang ya ce “godiya ga Allah babu ran da muka rasa.”

KU KARANTA KUMA: Kungiyar NLC ta bukaci ayi kakkaba a majalisar Buhari

Yayi bayanin cewa iskar da ake amfani da shi wajen girki ‘Cooking Gas’ da turanci ne ta fashe wanda hakan ya tada da gobarar.

Ya ce duk da cewa hukumar makarantan ta kafa dokar hana yin girki a dakunan kwanan daliban domin guje wa irin hakan amma taurin kan wasu daliban ya suka karya dokar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa

Gangamin PDP: Nyesom Wike da Uche Secondus sun kai wa Bode George ziyara a gidan sa
NAIJ.com
Mailfire view pixel