Dandalin Kannywood: Ba zan taba auren dan fim ba - Nafisa Abdullahi

Dandalin Kannywood: Ba zan taba auren dan fim ba - Nafisa Abdullahi

Shahararriyar yar wasan Hausa din nan a masana'antar fina-finai ta Kannywood watau Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa ita ba zata auri dan fim ba ko wanene don tana da masoya da dama kuma a ciki ma har ta fitar da wanda take so.

Jarumar tayi wannan ikirarin ne a cikin wata fira da tayi da majiyar mu yayin da take ansa tambayoyi daga wakilin na majiyar.

Dandalin Kannywood: Ba zan taba auren dan fim ba - Nafisa Abdullahi
Dandalin Kannywood: Ba zan taba auren dan fim ba - Nafisa Abdullahi

Legit.ng ta samu cewa da aka tambaye ta kuma ko me gaskiyar labarin cewa an sa mata biki amma sai ka kuma fasa, sai jarumar ta kada baki tace ita dai a iya sanin ta ba ta san da wannan maganar ba amma watakila masu maganar su ne suka sa mata bikin.

Ta ci gaba da cewa ita dai abun da ta sani shine ta na masoya da dama kuma ita tun tuni ta fitar da wanda take so kuma shi zata aura cikin izinin Allah a nan gaba kadan kuma ta kara da cewa shi din ba dan fim bane.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel