Buhari: Dalilin da yasa ban halarci taron gwamnoni da Buhari ba – Fayose

Buhari: Dalilin da yasa ban halarci taron gwamnoni da Buhari ba – Fayose

- Gwamnan jihar Ekiti ya bayyana dalilin da yasa bai samu halartar taron ganawa tsakanin gwamnonin da shugaban kasar ba

- Gwamnan ya karyata zargin cewa da gangan yaki halartar ganawar da shugaban kasa

- Fayose ya ce a wannan ranar za a nada shi sarauta na gargajiya a matsayin Apesin na Ado Ekiti

Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya bayyana dalilin da yasa bai samu damar halartar taron ganawa tsakanin gwamnonin kasar da shugaba Muhammadu Buhari ba.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Fayose ya ce ba zai iya barin wani taron da ya shirya ba don halartar taron ganawa da shugaba Muhammadu Buhari a Abuja ba. Gwamnan ya nuna rashin amincewarsa da maganganun mutane cewa da gangan yaki halartar ganawar a ranar Juma'a tare sauran gwamnonin.

A cikin jerin maganarsa a shafinsa ta Twitter, Mista Fayose ya ce ya samu takadar gayyatar zuwa ganawa da shugaban kasar, amma kuma a wannan ranar za a yi masa nadin sarauta na gargajiya a matsayin Apesin na Ado Ekiti. Ya ce a matsayinsa ba zai iya kaurace wa taron ba saboda taron ganawa da shugaban.

Buhari: Dalilin da yasa ban halarci taron gwamnonin da Buhari ba – Fayose

Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose a bikin nadin sarauta

Ya ce mutane da dama sun riga sun kasance a Ekiti tun daga ranar Alhamis, 24 ga watan Agusta domin wannan nadin kafin in samu sanarwar ganawa da shugaban kasar.

KU KARANTA: Labarai cikin Hotuna: Shugabannin jam'iyyun APC da PDP sun kaiwa Shugaba Buhari ziyarar ban gajiya

“Babu yadda zan iya barin bakin da suka zo nan Ado Ekiti don taya ni murna saboda ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ", inji Fayose a cikin rubutunsa.

Bayan ganawa da gwamnonin jihohi, shugaba Buhari ya kuma sadu da jagorancin manyan jam'iyyun biyu, APC da PDP a fadar shugabn kasa da ke babban birnin tarayya ta Abuja.

Taron ta samu halartar mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da shugaban jam’iyyar APC, John Odigie-Oyegun da kuma shugaban jam'iyyar adawa ta PDP, sanata Ahmed Makarfi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar

Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar

Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar
NAIJ.com
Mailfire view pixel