Ojukwu ya gaskata maganar da Buhari yayi na ganawa da mahaifinsa san da yana raye

Ojukwu ya gaskata maganar da Buhari yayi na ganawa da mahaifinsa san da yana raye

- Dan gidan marigayi Ojukwu ya gaskata maganar Buhari ta ganawa da mahaifinsa kan hadin kan kasar Najeriya

- Ojukwu ya shaidawa gidan jarida ba shi da hannu a zancen da ake yadawa ta shafukan sada zumunta na cewar ya musanta zancen shugaban kasa

- Yayi kira ga shugaban kasa yayi watsi da duk masu son su kawo batanci a mulkinsa

Dan gidan marigayi Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, Emeka Ojukwu a jiya yayi Allah wadai da 'yan goyon bayan Bayafara, ya gaskata maganar da shugaba Buhari yayi a ranar litinin na cewar 'ya tattauna da mahaifinsa akan hadin kan kasara Najeriya.'

Ojukwu ya shaidawa gidan jarida cewar bai bawa kowace gidan jarida dama ko ya rubuta a shafukansa na sada zumunta cewar maganar da Buhari yayi da mahaifinsa ba gaskiya bace.

Ojukwu ya gaskata maganar Buhari ta ganawa da mahaifinsa

Ojukwu ya gaskata maganar Buhari ta ganawa da mahaifinsa

A kafofin sada zumunta ne wasu suke yada zancen Ojukwu ya karyata maganar Buhari da yayi da marigayi Ojukwu ta Najeriya zata zama kasa guda daya bazata rabe ba.

Ojukwu ya kara da tabbatar da cewa lallai mahaifinsa ya gana da Buhari san da yana raye kuma duk abubuwan da Buhari ya fadi sun tattauna gaskiya ne. Sannan kuma yace 'zancen da aka ce yayi a shafukan yanar gizo ba gaskiya bane'.

DUBA WANNAN: Gwamnati Zata Kashe Biliyan 3 don Farfado Da Ilimi A Arewa

Yana mai kara yiwa shugaban kasa maraba da dawowa gida Najeriya. Da bukatar shugaba Buhari yayi watsi da duk wasu masu irin wannan maganganun a harkar Shugabancinsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel