Gwamnonin kudancin Najeriya sun bayyana cikakken goyon bayan su ga Buhari

Gwamnonin kudancin Najeriya sun bayyana cikakken goyon bayan su ga Buhari

Gamayyar hadakar gwamnonin jihohi sha-daya daga yankunan kudancin kasar nan da suka hada da kudu maso kudu da kuma kudu maso arewa a jiya sun fitar da sanarwa inda suka kara jaddada cikakken goyon bayan su ga shugaba Buhari da kuma kudurorin gwamnatin sa.

Kungiyar ta fitar da sanarwar ne a cikin wata takardar manema labarai da shugaban ta gwamnan jihar Akwa Ibom Mista Udom Emanuel ya ya sanyawa hannu a madadin takwarorin sa.

Gwamnonin kudancin Najeriya sun bayyana cikakken goyon bayan su ga Buhari

Gwamnonin kudancin Najeriya sun bayyana cikakken goyon bayan su ga Buhari

NAIJ.com ta samu cewa takardar na kuma kunshe da gaisuwa da bangajiya da kuma godiya ga Allah da ya maido sa gida lafiya tare da kuma rokon Allah ya kara masa lafiya domin cigaba da mulkin sa.

Daga karshe ne kuma sai takardar ta kara jaddada goyen baya ga shugaban daga gwamnonin na yankuna biyun tare kuma da tabbatar da hadin kan su ga Gwamnatin tasa a dukkan lamuran da za su kawo ci gaba.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel