Yanzu Yanzu: An sanar da 1 ga watan Satumba a matsayin ranar Eid-el-Kabir

Yanzu Yanzu: An sanar da 1 ga watan Satumba a matsayin ranar Eid-el-Kabir

Sarkin Musulmi, Sultan na Sokoto, Alhaji Sa’ad Abubakar ya sanar da ranar 1 ga watan Satumba a matsayin ranar babban Sallah wato Eid-el-Kabir.

Hakan na dauke ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun farfesa Sambo Junaidu, shugaban kungiyar mashawarta a kan harkokin addini na masarautar jihar Sokoto.

Sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ta samu a jihar Sokoto a ranar Laraba, ya nuna cewa sanarwar ya biyo bayan ganin sabon water Zulhijja da akayi a ranar Talata, 22 ga watan Agusta.

Sanarwar ta bayyana cewa Musulman Najeriya zasu gudanar da bikin babban Sallah a ranar Juma’a 1 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: Beraye ma sun ki ka – Dokubo ya fada ma Buhari

Ya kara da cewa Sultan na yi wa Musulmai fatan alkhairi da kuma kariya daga Allah.

sanarwar ta kuma bayyana cewa Abubakar ya bukaci musulmai da su ci gaba da zama cikin zaman lafiya da kuma addu’a don ci gaban kasar da ma duniya baki daya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel