Beraye ma sun ki ka – Dokubo ya fada ma Buhari

Beraye ma sun ki ka – Dokubo ya fada ma Buhari

- Tsohon shugaban yan bindiga, Asari Dokubo, ya bayyana mamayar beraye a ofishin shugaba Buhari a matsayin abun kunya

- Dokubo yace mamaya da beraye suka yi a ofishin Shugaban kasa alama ne na kin shi da aka yi

Tsohon Shugaban yan bindiga, Asari Dokubo, yayi wa shugaba Muhammadu Buhari ba’aa kan rahoto da aka gabatar cewa beraye sun addabi ofishin shi.

NAIJ.com ta tuna cewa mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu a ranar Talata, 22 ga watan Agusta, yace beraye sun lalata wasu muhimman takardu a ofishin Buhari saboda hakan ne shugaban zai dunga gudanar da aikida ga gida.

Dokubo ya bayyana ra’ayin shi game da Jawabin Garba Shehu a wani bidiyo da aka gabatar a 23 ga watan Agusta, inda ya bayyana mamayar beraye a ofishin Buhari abun kunya.

Kalli bidiyon a kasa:

Tsohon dan bindigan, yayi Magana cikin Karin magana, cewa Beraye sun kori zaki daga ofis.

KU KARANTA KUMA: Wa’adin barin gari: Fadar shugaban kasa ta gana da matasan Arewa

Dokubo yace berayen sun kasance alaman kin shi a matsayin Shugaban kasa.

Haka zalika, BBC tayi wa Najeriya ba’a ranar Laraba, 22 ga watan Agusta kan bayanai da aka yi cewa beraye sun kori shugaban kasa daga ofis.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel