Gwamnatin jihar Kwara ta kashe N7bn akan aikin hanya a cikin shekara guda

Gwamnatin jihar Kwara ta kashe N7bn akan aikin hanya a cikin shekara guda

Gwamnatin Kwara a ranar talata ya ce ya kashe kimanin N7bn a samar da hanyoyi, tun daga watan Satumba 2016 lokacin da aka kaddamar da shirin gudanar da asusun tallafi (IF-K).

Kwamishinan ayyuka da sufuri na jihar, Alhaji Aro Yahaya ya bayyana hakan a Ilorin lokacin da yake jawabi a majalissar na kungiyar 'yan jaridar Najeriya (NUJ).

Yahaya ya bayyana cewa asusun ya taimaka wa jihar wajen kammala ayyukan hanyoyi da kuma sabobbin hanyoyi wadanda aka amince.

Gwamnatin jihar Kwara ta ciyar da N7bn akan aikin hanya a cikin shekara guda

Gwamnatin jihar Kwara ta ciyar da N7bn akan aikin hanya a cikin shekara guda

KU KARANTA KUMA: An haifi wani jariri da juna biyu a kasar Indiya

Kwamishinan ya tabbatar wa mutanen jihar cewa za a kammala duk ayyukan kafin gwamnatin yanzu ya gama mulkin sa a jihar.

Ya bayyana cewa, mafi yawan masu kwangila da ke tafiyar da ayyuka a hanyoyi daban-daban na jihar sun watsar da aikin kafin su gano asusun IF-K a shekara ta 2016.

Kwamishinan ya ce za a kammala aikin da akeyi a hanyar Geri-Alimi a Ilorin a cikin watanni 12 masu zuwa,wanda zai taimaka wajen saukin tafiyar da motoci a hanyar.(NAN).

Idan ka na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel