Yanzu-Yanzu: Buhari zai rubutawa majalisar tarayya takarda, ya ce masu ya dawo da kwarin sa

Yanzu-Yanzu: Buhari zai rubutawa majalisar tarayya takarda, ya ce masu ya dawo da kwarin sa

Labaran da muke samu yanzu ba da dadewa ba suna nuni da cewa a yau din nan ne dai ake sa ran shugaba Buhari zai rubutawa majalisar tarayya da suka hada da majalisar dattijai da kuma wakillai domin sanar da su dawowar sa a hukumance kasar don ya ci gaba da mulki.

Ana dai sa ran cewa shugaban zai fadawa majalisun a rubuce cewa ya dawo kasar cikin koshin lafiya bayan da ya shafi fiye da watanni uku yana jinya a kasar Ingila a kuma birnin Landan.

Yanzu-Yanzu: Buhari zai rubutawa majalisar tarayya takarda, ya ce masu ya dawo da kwarin sa

Yanzu-Yanzu: Buhari zai rubutawa majalisar tarayya takarda, ya ce masu ya dawo da kwarin sa

NAIJ.com ta tuna cewa a cikin satin da ya wuce ma dai shugabannin majalisun na tarayya da suka hada da shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki da kuma kakakin majalisar wakillai Honarable Yakubu Dogara sun ziyarci shugaba a inda yake jinya.

Tun bayan dawowar sa dai shugaban ya amshi kayyawar tarba daga kowane sashe na tarayyar kasar inda kuma yau da safe ya yi jawabi mai ratsa zuciya ga daukacin yan kasar.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel