Yan bindiga sun kashe mataimakin Gwamna Samuel Ortom

Yan bindiga sun kashe mataimakin Gwamna Samuel Ortom

-Yan bindigan sun harbe shi ne a cikin gida shi

-Sun harbi matan sa amma bata mutu ba

-Gwaman jihar yayi alkwarin taimaka wa jam'ian tsaro wajen kamo wadanda suka yi kisan

Yan Bindiga sun harbe mai ba Gwamna jihar Binuwai shawar akan Tattalin Arziki da Harkokin Kasuwanci, Dokta Tavershima Adyorough,inda suka samu nasarar kashe a gidan sa da misalin 12.30pm na ranar Lahadi 20 ga watan Agusta 2017.

Yan bindigan sun harbi matar shi , amma it bata mutu ba ta na karkashin kulawan likitoci a asibiti.

Yan bindiga sun kashe mataimakin Gwamna Samuel Ortom

Yan bindiga sun kashe mataimakin Gwamna Samuel Ortom

Gwamnan,Ortom yayi Allah wadai da kisan da akayi kuma ya nuna rashin yarda sa , ya kuma umarci jam’ian tsaro da su tsananta bincike dan gano wadanda suka aikata wannan mumunan al’amari.

A jawabi gwamnan ta mai magana da yawon bakin sa, gwamnan yace marigayin Mista Terver Akase mutum ne mai gaskiya da rikon amana kuma yana jajircewa wajen yin aikin shi.

KU KARANTA:Hukumar 'Yansanda ta bankado matsafa da ake yankan kan yara

Gwamnan ya mika ta’azaiyar sa zuwa ga iyalin mamacin, da gwamantin da kuma mutanen jihar. Ya yayi alkawarin taimakawa jam’ian tsaro wajen kama wadanda suka aikata ta’adancin.

Yayi kira da al’umma jihar da su taimaka wa jam’ian tsaro da dukkan bayyanai da zai taimakawa wajen kama wadanda suka yi kisan.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel