Batutuwan da ya kamata Buhari ya bayyanawa 'Yan Najeriya

Batutuwan da ya kamata Buhari ya bayyanawa 'Yan Najeriya

- Ranar Litinin Shugaba Buhari zai yi wa 'Yan Najeriya jawabi

- Jaridar The Cable ta kawo abubuwan da ya kamata a ji

- Tace ya dace Shugaba Buhari yayi magana game da wasu batu 5

Jama'ar kasar sun tasa kunne ana jiran lokacin yayi domin Shugaban kasa yayi jawabi. Kowa dai yana jira domin jin abin sa Shugaban kasar zai fada a safiyar Litinin.

Batutuwan da ya kamata Buhari ya bayyanawa 'Yan Najeriya

Shugaba Buhari ya shigo Najeriya

Jaridar The Cable ta kawo abubuwan da ya kamata a ji daga bakin Shugaban kasar:

KU KARANTA: Sarakunan Ibo sun yi murnar ganin Buhari

1. Maganar guba

A wancan karo Shugaban kasar yace ba guba ya ci ba. Akwai dai wannan jita-jitar kuma ya kamata a san abin da ake ciki.

2. Maganar hadin kai

Bayan tafiyar Shugaban kasar ana ta barazanar raba kasar. Mukaddashin Shugaban kasar yayi taro da Jama'a daga Yankunan amma har yanzu akwai sauran aiki.

3. Maganar Sakataren Gwamnati

Daf da tafiyar Shugaba Buhari ya sa ayi bincike game da Sakataren Gwamnatin Tarayya da Shugaban Hukumar NIA wanda har yanzu ba a san inda ake cika ba.

Batutuwan da ya kamata Buhari ya bayyanawa 'Yan Najeriya

Wasu 'Yan Najeriya na kira a raba kasar

4. Boko Haram

Ba shakka 'Yan Kungiyar Boko Haram sun dawo da dan karfin su. Za a so shi ma a ji irin tanadin da Shugaban kasar zai yi masu.

5. Tattalin arziki

Jaridar tace akwai dacewar Shugaba Buhari ya bayyanawa Duniya inda ya sa gaba wajen harkar tattalin arziki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Gwamnan Katsina yayi murnar dawowar Buhari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel