2019: Dalilin da yasa PDP bata yanke shawaran tsayar da Fayose a matsayin dan takaran shugaban kasa ba-Makarfi

2019: Dalilin da yasa PDP bata yanke shawaran tsayar da Fayose a matsayin dan takaran shugaban kasa ba-Makarfi

-A lokacin da zamu yi taron ne na zamu tsayar da dan takara

-Ba Fayose kadai bane ya nuna ra'ayin tsayawa takara

-Babu wata gaba a tsakanina da Sheriff-Makarfi

Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar PDP, senata Ahemd Makarfi yace jam’iyyar sa za ta bayyana matsyinta game da kudirin Ayodele Fayose na tsayawa takaran shugaban kasa.

NAIJ.com ta rawaito cewa a mako biyu da suka gabata ne Ayodele Fayose ya bayyana niyya sa na tsaya takarar shugaban kasa a lokacin babban taron da Jam’iyya ta tayi a Abuja.

A lokacin da Makarfi yake zantawa da manema labarai na Jaridan Punch,yace jam’iyyar su ba ta yanke shawaran tsayar da kowa ba, sai lokacin da zu su yi babban su taron na siyasa.

2019: Dalilin da yasa PDP bata yanke shawaran tsayar da Fayose a matsayin dan takaran shugaban kasa ba-Makarfi.

2019: Dalilin da yasa PDP bata yanke shawaran tsayar da Fayose a matsayin dan takaran shugaban kasa ba-Makarfi.

Ya kara dacewa,“akwai mutane dayawa da suka nuna sha’awan tsayawa takaran shugaban kasa lokacin taron su da yagabata. Ba Fayose kadai bane, akwai tsofaffin gwamnoni guda 2 da suka fitar da fostocin na nuna ra’ayin tsayawa takara. Taron da aka yi a baya, ba na nuna goyon bayan kowa bane.

KU KARANTA:Hukumar 'Yansanda ta bankado matsafa da ake yankan kan yara

“Harda fostocin wasu da kai da ra’ayin tsayawa takaran gwamna da sauran mukamai. Wannan bai nuna muna goyon bayan kowa ba”.

Akan rikicin shugabanci dake tsakanin su da Ali Modu Sherrif, Shugaban jam’iyyar PDP na yanzu yace babu wata gaba a tsakanin su da Sherrif.

Makarfi, tsohon gwamnan jihar Kaduna yace jam’iyyar ba za ta kori Sherrif ba sai dai in ya yanke shawarar fita daga jam’iyan.

Ya kara da cewa,“Ba mu bane za mu yanke shi shawara. Ra’ayin shine. Mutanen shi da dama sun halarci taron da muka yi. Kuma wasu daga cikin mutanen shi su yi aiki a kwamitoci da dama a lokacin taron.Kowa yana da ikon bin ra’ayin shi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel