Yadda Zahra Buhari da abin kaunarta Ahmed Indimi suke sharholiyyar su a kasashen ketare

Yadda Zahra Buhari da abin kaunarta Ahmed Indimi suke sharholiyyar su a kasashen ketare

Kuturu da kudin sa, alkaki sai na kasan kwano domin kuwa Zahra Buhari da abin kaunarta kuma mijin ta suna yadda suke so kuma dama ance duk wanda ya samu rana sai yayi shanya

A watannin da suka gabata, shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya aurawa wani hamshakin mai kudi na jihar Borno, Ahmed Indimi 'yar sa Zahra Buhari inda aka yi biki na kece raini.

Yadda Zahra Buhari da abin kaunarta Ahmed Indim suke sharholiyyar su

Yadda Zahra Buhari da abin kaunarta Ahmed Indim suke sharholiyyar su

Gagarimin bikin auren na su ya dauki tsawon lokuta ana tattaunawa da tafka muhawarori akai, sanadiyar irin yadda kudi wanda hausawa ke cewa masu gidan rana suka yi ranar a wannan lokaci.

Daga ire-iren kayan aure na tufafi, sha'ani da kuma abinci wanda mutum zai lasa a bakinsa, abin dai ba a cewa komai domin kuwa gani aka ce ya kori ji don kuwa har kwanan gobe kowace yarinya za ta so samun irin wannan daula wajen aurenta.

KU KARANTA: Shugaba Muhammadu Buhari zai dawo yau asabar – Femi Adesina

Kashe kudi da holewa bai tsaya a auren na su kadai ba, domin kuwa kawowa yanzu, Zahra da mijin na ta suna zageyen kasashen duniya inda duk wani waje na shakatawa yake su na halarta.

Wayyo dadi! Domin kuwa hotunan Zahra da mijin ta suna kewaye kafofin labarai da dandalai na sada zumunta akan irin shakatawa da annusha da suke samun a tsakiyar teku cikin wani jirgin ruwa na alfarma.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel