Siyasar Kaduna: Wata kungiya ta baiwa jama'ar Kaduna hakuri saboda mara wa El-Rufai baya da tayi

Siyasar Kaduna: Wata kungiya ta baiwa jama'ar Kaduna hakuri saboda mara wa El-Rufai baya da tayi

- Malam Nasir El-Rufai na fuskantar zafafan suka daga 'yan siyasa na jihar, dalilinsu wai tunda ya ci zabe yayi watsin tsiwa da su, sun sha alwaashin ramuwa a zabe mai zuwa, muddin ya ce zai sake tsayawa takara.

Wata kungiya mai suna 'Concerned Southern Kaduna APC Youths' tayi nadamar zaben gwamna El-Rufai kuma har ila yau ta nemi gafaran mutanen jihar domin rawan ta suka taka wajen tabbatar da cewa El Rufai ya ci zama gwamnan jihar Kaduna.

Siyasar Kaduna: Wata kungiya ta baiwa jama'ar Kaduna hakuri saboda mara wa El-Rufai baya da tayi

Siyasar Kaduna: Wata kungiya ta baiwa jama'ar Kaduna hakuri saboda mara wa El-Rufai baya da tayi

Kungiyar tace basuyi tsamanin zai yi musu irin abubuwan musgunawa da yake musu ba, a cewarsu, ya hana mutane, malaman addinin da masu mulkin gargajiya sakat, hakan baya cikin alkawarin da yayi musu gabannin zaben.

A cikin sanarwan da shugaban kungiyan, Honorable Victor Akat ya bada, yace basu taba shiga mummunan hali irin wannan ba a rayuwarsu.

"Ko makafi da bebaye zasu iya fahimtar irin rashin adalci ya gwamna yake yi wajen warware matsalar jami'an jihar kaduna da ke yankin mu, ya kule jami'an kuma ya hana masu kasuwanci a harabar jami'an hanyan samun abinci"

"Muna matukan bakin ciki idan muka tuna cewa da hannun mu muka zabe shi, abubuwan da yake aikatawa ba komai bane face dakile cigaban yaran mu, muna fata yaran mu zasu jure yar wannan wahalar domin nan da lokaci kadan mulkin nasa zai zo karshe". Inji Akat.

"Muna neman afuwan sarakunan yankin mu da suka rasa kujerar mulkin su, bamu da sanin gaibu shi yasa muka zabe shi, muna addua Ubangiji ya kawo wata sabuwar gwamnati da ke sauraran koke-koken jama'a"

DUBA WANNAN: Gawar Suntai ta isa makwanci cikin hawaye (Hotuna)

"Hakin gwamnati ne kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin kasa ta kare rai, lafiya da dukiyoyin jama'a amma abin takaici mutanen Birnin Gwari suna cikin fargaba domin yan bindiga dadi da masu garkuwa da mutane sun sa su a gaba, babban titin Kaduna-Abuja ma ya zama matattaran yan fashi da makami da masu garkuwan da mutane." Bayanin ya rufe.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel