Buhari zai yiwa 'yan Najeriya jawabi a ranar Litinin

Buhari zai yiwa 'yan Najeriya jawabi a ranar Litinin

Ana sa rai da cewar shugaba Buhari zai yiwa kasa Najeriya jawabai a ranar Litinin daidai da 21 ga watan Agusta da misalin karfe 7:00 na safe.

A yau asabar 19 ga watan Agusta, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dawo gida Najeriya bayan fiye da kwananki 100 da ya shafe a birnin Landan yana jinya.

Buhari zai yiwa 'yan Najeriya jawabi a ranar Litinin

Buhari zai yiwa 'yan Najeriya jawabi a ranar Litinin

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa da manema labarai a safiyar yau Asabar kuma zai yiwa al'umma kasa baki daya jawabi a ranar Litinin 12 ga watan Agusta da misalin karfe 7:00 na safe.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun cafke wani mutum da kan wata mace a jihar Legas

Shugaba Buhari ya bar kasar nan ne a ranar 7 ga watan Mayu, inda ya mika ragamar shugabancin Najeriya a hannun mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin mukaddashi.

Adesina ya ce, ana sa ran zai dawo kasar nan a yau Asabar kuma zuwa safiyar ranar Litinin 21 ga watan Agusta da misalin karfe 7:00 zai yiwa 'yan Najeriya jawabai.

Ya kara da cewa, shugaba Buhari yana miko gaisuwa da kuma godiya ga duk 'yan Najeriya da suka dukufa wajen yi ma sa addu'a akan ya samu waraka tun daga lokacin da ya kwanta jinya.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel