Ana zargin wani Fasto da yaudarar kudi ta Naira miliyan 1.7

Ana zargin wani Fasto da yaudarar kudi ta Naira miliyan 1.7

Daman dai ance ba a yabon dan kuturu domin kuwa wani fasto ya gurfana da laifin cin amanar kudi gar Naira miliyan daya da dubu dari bakwai a jihar Benuwe

A ranar juma'ar da gabata ne wani tsohon Fasto mai shekaru 43, Uchenna Okafor, ya gurfana a gaban wata kotun Majistare domin hukunci, inda ake zargi sa da cin amanar kudi na wani mamba a cocin sa har Naira miliyan daya da dubu dari bakwai.

Okafor yana fuskantar nau'i biyu na laifin da ya aikata na cin amina da kuma wawushen kudin da ba na sa ba wanda ya sabawa dokar sashe na 310 da 313 na dokokin jihar Benue.

Jami'in dan sanda mai gabatar da kara, Godwin Ato, ya shaidawa kotu cewa an bayar da wata takarda a ranar 1 ga watan Agustan daga cibiyar bincike ta jiha (State Criminal Investigations Department, CID) ta Makurdi, wanda mai tuhuma Peter Irokwende ya rubuto.

Ana zargin wani Fasto da yaudarar kudi ta Naira miliyan 1.7

Ana zargin wani Fasto da yaudarar kudi ta Naira miliyan 1.7

Mai tuhumar ya bayyana cewa an sayar da gonar zuwa ga Uchenna Iroegbu a kan Naira miliyan daya da dubu dari bakwai.

KU KARANTA KUMA:Amfanin ayaba guda 7 a jikin mutum

Iroegbu ya ce ya karbi lambar asusun fasto ta banki kamar haka; 4703061956 a Eco Bank, dauke da sunan Uchenna Livinus Okafor don biyan wannan kudi.

Mai tuhumar ya bayyana cewa mai siyan gonar ya biya wannan kudi cikin asusun banki, inda a cewar shi "wannan fasto ya haye kan wannan kudade domin biyan bukatun sa, kuma ya ce shi sam wannan bazai baiwa Livinus wannan kudi ba"

Kotu ba ta tabbatar da laifin wannan Fasto ba, sai dai alkali mai shari'a, Isaac Ajim ya bayar damar a yi beli da kudi naira 50, 000 kuma ya daga sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Agusta.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel