Wata mata ta dilmiya jaririn ta mai kwanaki 3 a duniya cikin ruwa

Wata mata ta dilmiya jaririn ta mai kwanaki 3 a duniya cikin ruwa

Rashin tausayi da rashin sanin ya kamata ya sanya wata mata a jihar Nassarawa ta dilmiyar da jaririn ta mai kwanaki 3 a duniya cikin ruwa kuma ta shiga hannun hukuma sanadiyar wannan ta'addancin

'Yan sandan jihar Nasarawa sun kama wata mata mai shekaru 25 da ake kira Mwuese Keleve, wadda ake zarginta da kashe jaririn ta mai kwanaki 3 kacal a duniya a wani yankin Kadarko na karamar hukumar Keana a jihar.

Rundunar 'yan sanda sun bayyana cewa, a ranar Litinin din da ta gabata ne, su ka samu rahoto game da gawar jaririn da aka samu a gabar wani kogi a yankin.

Kakakin 'yan sandan jihar, DSP Idirisu Kennedy, ya shaidawa kamfanin jaridar labaran arewa na babban birnin Lafia cewa, an kama mahaifiyar jaririn ne a ranar Talata ta makon da ya gabata.

Wata mata ta dilmiya jaririn ta mai kwanaki 3 a duniya cikin ruwa

Wata mata ta dilmiya jaririn ta mai kwanaki 3 a duniya cikin ruwa

Ya kara da cewa, wadda ake tuhuma ta amsa aikata wannan laifin kuma ba tare da wani dalilin da ya sa ta kashe jaririn ba kuma ta na da cikakkiyar lafiyar hankali.

Kennedy ya ce za a gurfanar da Keleve a gaban kotu da zarar 'yan sanda suka kammala binciken su.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun cafke wani mutum da kan wata mace a jihar Legas

Shi kuwa mijin wannan mata, Fanen Peter, ya ce abin da matarsa ​​ta yi ya jefa shi cikin mamaki, domin kuwa ya ce sun yi aure tun shekaru 15 baya har da 'ya'ya biyu kuma marigayin shine dan su na uku.

Da yake jawabi a kan lamarin, sarkin yankin na su, Kadoko na Kadarko, Cif Fabian Orugu, ya bayyana aikin da Keleve ta yi a matsayin aikin shaidan wanda ba zai iya jurewa ba.

Ya kuma yaba da kokarin da mazauna yankin da 'yan sanda suke yi donwajen haɗin kai wanda sanadiyar hakan ne aka yi nasarar damke wannan mata.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel