Katsina: Wani gwamna Arewa ya bayyana abin da yasa yaki da cin hanci da rashawa ke da wuya a Najeriya

Katsina: Wani gwamna Arewa ya bayyana abin da yasa yaki da cin hanci da rashawa ke da wuya a Najeriya

- Gwamnan jihar Katsina ya ce yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya nada yuwa sosai

- Masari ya zargi lauyoyi n kasar nan cewa sun kasa aikata abubuwan da suka dace

- Gwamnan ya yiwa NBA alkawarin kyautar motar bas da filin da za su gina ofisoshin ta

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya koka cewa, yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya na zama abu mai wuya.

Gwamnan ya zargi lauyoyi game da halin da ake ciki, yana cewa sun kasa aikata abubuwan da suka dace.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Masari, ya yi wannan magana ne a lokacin da ya karbi bakoncin tawagar 'yan kungiyar lauyoyi na Najeriya, NBA, shiyar jihar Katsina a fadar gwamnati.

Katsina: Wani gwamna Arewa ya bayyana abin da yasa yaki da cin hanci da rashawa ke da wuya a Najeriya

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari

Masari ya ce: "Ya kamata lauyoyin Najeriya su kasance a gaba a kan kare gaskiya, ba kawai a kotu ba, amma a kan abin da ke daidai ga yawancin jama'a. Ya kamata ku kasance a gaba don canza abin da ba dai dai ba, musamman a wannan lokaci mai muhimmanci a ci gaban wannan ƙasar".

KU KARANTA: Lauretta Onochie ta caccaki tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

“Lauyoyi na da babban rawar da za su taka, a gaskiya ma, fiye da kowane. Wannan shi ne saboda mutane suna ganin za su iya samu adalci a kotu", inji gwamnan.

A lokacin da ‘yan kungiyar NBA suka nema taimakon kudi don tallafawa ayyukan kungiyar, Masari ya bukaci ƙungiyar ta gabatar da kasafin kudinta na shekara cewa gwamnatinsa za ta taimaka musu.

Gwamna ya kuma tabbatar wa NBA cewa gwamnatin jihar za ta ba su sabuwar motar bas da kuma fili don gina ofisoshin su a Katsina da Funtua.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel