Lauretta Onochie ta caccaki tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

Lauretta Onochie ta caccaki tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

- Hadimar shugaba Buhari, Lauretta ta caccaki tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

- Lauretta tace kamata yayi ace ya ja gwiwowinsa daga kauyensa Otueke zuwa Kaura Namoda, don ba kasar Najeriya hakuri kan yadda ya wawashe ta

- Ta ce gwamnatin Jonathan ta cika da tarin alkawara na karya, rashawa da kuma rusassun mafarkai

A ranar Talata, 15 ga watan Agusta, mataimakiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta musamman a shafukan zumunta, Lauretta Onochie ta caccaki tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a shafinta na twitter,

Hadimar shugaban kasar ta bayyana cewa kamata yayi ace ya ja gwiwowinsa daga kauyensa Otueke zuwa Kaura Namoda, don ba kasar Najeriya hakuri kan yadda ya wawashe ta.

Ta ce gwamnatin tsohon shugaban kasa Jonathan ta cika da tarin alkawara na karya, rashawa da kuma rusassun mafarkai.

Lauretta Onochie ta caccaki tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

Lauretta Onochie ta caccaki tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Mutane 3 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Abuja

A cewarta, gwamnatin Buhari tafi ta Jonathan sau dubu, kamar yadda Buhari ya yi abunda ba’a taba yi ba a tarihi na sanya yara cikin amfana daga kasar.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel