Watanni 8 a gidan Kaso – Wani mutum ya saci buhu 90 na siminti

Watanni 8 a gidan Kaso – Wani mutum ya saci buhu 90 na siminti

Kowa dai da kiwon da ya karbe shi domin wani barawo a jihar Ondo ya saci buhu 90 na siminti na kimanin kudi Naira 229, 500

Wata kotun majistire a jihar Ogun, ta yankewa wani mutum, Anthony Ukpe, mai shekaru 45 a duniya, hukuncin zama a gidan kaso har na tsawon watanni 8 sanadiyar satar buhu 90 na siminti wanda kudin su ya kai Naira 229, 500.

Alkali mai shari’a, S. O Banwo, wanda ya zartar da wannan hukuncin, bai bayar da wata dama ba ta biyan diyya a madadin zaman gidan kaso.

Ukpe wanda ya ki bayyana mazaunar sa, ya gurfana a gaban kotu ne da laifukan sata da tuggu wanda kuma ya amsa laifin na sa.

Watanni 8 a gidan Kaso – Wani mutum ya saci buhu 90 na siminti

Watanni 8 a gidan Kaso – Wani mutum ya saci buhu 90 na siminti

A baya can, jami’in dan sanda, Sajen Chudu Gbesi, ya bayyanawa kotu cewa, a ranar 15 ga watan Yuli, wannan mutum tare da wasu wadanda har yanzu ba su shiga hannu ba sun aikata wannan laifin ne a unguwar Onhale ta karamar hukumar Ota a ta jihar Ogun.

KU KARANTA: Kiwon Lafiya: Dalilai da za su sanya kara riko da abarba

Gbesi ya ce, wannan mutumin tare da makarraban sa, sun sacewa wani Fatoki Sunday buhunan siminti guda 90 wanda jimillar kudin su ta kai Naira 229, 500.

Ya kara da cewa, wannan laifin ya sabawa sashe na 426 da 516 na dokokin aikata miyagun laifuka bugun farko na dokokin jihar Ogun.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel