Boko Haram: An bukaci gwamnatin tarayya da ta inganta matakan tsaro don kare ‘yan gudun hijira

Boko Haram: An bukaci gwamnatin tarayya da ta inganta matakan tsaro don kare ‘yan gudun hijira

Hukumar dake jin kan jama’a ta duniya, tace ya zama lallai gwamnatin tarayyan Najeriya ta tsaurara matakan tsaro don kare lafiyar yan gudun hijira da yan ta’addan Boko Haram suka raba das u da walwalarsu.

Hakan ya biyo bayan hallaka mutane 28 da yan taáddan suka yi a wani mummunan hari da suka kai sansanin yan gudun hijira a ranar Talata, 15 ga watan Agusta.

A cewar hukumar, sansanin ‘yan gudun hijira, wani tudun mun-tsira ne ga mutanen da su ka guje wa tashin hankali, amma saboda sakaci an maida shi wurin dana tarkon kisa.

Shugaban hukumar reshen Najariya Ernest Mutanga ya ce, su na bukatar gwamnatin tarayya da ta kara kaimi wajen kare rayukan fararen hula dake samun mafaka a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Boko Haram: An bukaci gwamnatin tarayya da ta inganta matakan tsaro don kare ‘yan gudun hijira

Boko Haram: An bukaci gwamnatin tarayya da ta inganta matakan tsaro don kare ‘yan gudun hijira

A baya NAIJ.com ta rahoto cewa yan kwanaki bayan ba rundunar soji a arewa maso gabas kwanaki 40 su kamo Abubakar Shekau a raye, shugaban kungiyar na Boko Haram ya saki sabon bidiyo.

KU KARANTA KUMA: Rundunar soji sun kai ma yan Boko Haram harin bazata, sun kashe 10 (hotuna)

A cikin sabon bidiyon, Shekau ya yi ba’a ga shugaban kasa Muhammadu Buhar, da kuma tsohon shugaban kasa.

Ya kuma yi ba’a ga shugaban hafsan soji Tukur Buratai wanda ya ba da kwanaki 40 a kamo shi

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel