Wani kafinta ya gurfana a gaban kotu da laifin yunkurin satar mota

Wani kafinta ya gurfana a gaban kotu da laifin yunkurin satar mota

A can birnin Shehu kuma, wani kafinta ya shiga hannu sanadiyar laifi na yunkurin satar mota

A ranar talatar da ta gabata ne, wata kotun majistire a jihar Sakkwato ta gurfanar na da wani kafinta, Murtala Sa’idu, mai shekaru 37 bisa laifin yunkurin satar mota kirar Honda Civic.

Alkali mai shari’a, Abubakar Adamu, ya gurfanar da Mallam Murtala sanadiyar laifuka biyu na tuggu da yankurin satar mota da kotun ta ke tuhumar shi da su, wanda hakan ya sanya Alkalin ya daga sauraro karar zuwa ranar 20 ga watan Agusta.

Jami’in dan sanda, Insfeta Na’Allah Jibo, mai karar wanda ake tuhuma, ya bayyanawa kotu cewa, sun cafke kafintan ne a yayin da yake yanke wasu wayoyi ma su bayar da wuta na cikin motar domin ya samu damar arcewa da ita cikin sauki.

Wani kafinta ya gurfana a gaban kotu da laifin yunkurin satar mota

Wani kafinta ya gurfana a gaban kotu da laifin yunkurin satar mota

Jibo ya ce, wannan mota mai lamba BC 987 DKA, mallakin wani Umar Farouk ce, wanda ya ajiye ta a kofar gidan shi a yayin da ya cafke kafintan yana yunkurin tafka ta’asa.

KU KARANTA: Kiwon Lafiya: Dalilai da za su sanya kara riko da abarba

Ya kuma bayyanawa kotu cewa, wannan mai motar da kan shi ya kawo kara ofishin su na Unguwar Rogo a dake jihar ta Sokoto.

Ya kara da cewa, wannan laifi ya sabawa sashe na 95 a cikin kundin tsari na final kot.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel