Daga yanzu duk wani kalami na nuna tsana aikin ta'addanci ne - Inji Osinbajo

Daga yanzu duk wani kalami na nuna tsana aikin ta'addanci ne - Inji Osinbajo

- Gwamnatin tarayya ta yi kakkausan jawabi a kan duk wata magana ko rubutu da ka iya haddasa ko kara rura wutar kyama da tsana tsakanin yan Najeriya

- Yemi Osinbajo ne ya bayyana haka a wani taro a kan harkokin tattalin arziki

- Osinbajo ya yi gargadin cewa yin kalaman masu nuna kyama da tsana na barazana ga zaman lafiyar kasa

Gwamnatin tarayya ta yi kakkausan jawabi a kan duk wata magana ko rubutu da ka iya haddasa ko kara rura wutar kyama da tsana tsakanin yan Najeriya tare da bayyana cewar daga yanzu yin hakan dai dai yake da laifin ta'addanci.

Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne ya bayyana haka a wani taro a kan harkokin tattalin arziki. Jawabin na osinbajo na zuwa ne a dai dai lokacin da wutar kalaman tsana da nuna kyama tsakanin kabilu da yankunan Najeriya ke kara ruruwa musamman tsakanin kabilun Hausa da Igbo.

Daga yanzu duk wani kalami na nuna tsana aikin ta'addanci ne - Inji Osinbajo

Daga yanzu duk wani kalami na nuna tsana aikin ta'addanci ne - Inji Osinbajo

Osinbajo ya yi gargadin cewa yin kalaman masu nuna kyama da tsana na barazana ga zaman lafiyar kasa kuma yin shiru shugabanni kan hakan dai dai yake da nuna goyon bayan su yana mai nuni da yadda kin tsawatarwar shugabanni ta jawo barkewar rikincin kabilinci a rwanda da kisar yahudawa na Hitler.

KU KARANTA KUMA: Minista ya yi murabus saboda an dauke wuta na tsahon awanni a kasar Taiwan

A karshe yayi kira ga duk shuganni a kowane mataki na kasa da su yi kira ga zaman lafiya da nuna fushin su a kan duk wani mai yin wannan mummunar dabi'a ta nuna kyama da tsana ga wata kabila ko yanki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel