Sabbin nade-naden Osinbajo: Kanin Sanata da ya fadi jarrabawar darewa kujerar Sakatare ya dare kujerar

Sabbin nade-naden Osinbajo: Kanin Sanata da ya fadi jarrabawar darewa kujerar Sakatare ya dare kujerar

-Cikin Famanan Sakatare da Osibanjo yayi wa nadi, har da kanin Sanata Philip Aduda mai suna Gabriel Aduda wanda ya fadi jarrabawar karin matsayi a baya

-Gabriel Aduda yayi aiki da hukumar EFCC kafin yayi murabus a bisa dalilin fadi jarrabawar tasa

-Wata majiya tace bisa ga dukkan alamu Osibanjo bai da masaniya akan fadi jarrabawar Gabriel Aduda

A sabon labari da ke fitowa daga kafafen yada labarai, an sami bayanai dake nuna wai kanin wani Sanata mai suna Gabriel Aduda da ya fadi jarrabawar karin matsayi zuwa matsayin Famanan Sakatare, matsayi mafi girma a ma'aikatu, in banda Ministoci, ya sami kujerar, a sabbin nade nade da Osinbajo yayi makon jiya.

Sabbin nade-naden Osinbajo: Kanin Sanata da ya fadi jarrabawar darewa kujerar Sakatare ya dare kujerar

Sabbin nade-naden Osinbajo: Kanin Sanata da ya fadi jarrabawar darewa kujerar Sakatare ya dare kujerar

Idan bamu manta ba, a ranar 24 ga watan Mayu na shekarar 2014, jaridar Premium times ta kawo rahoto inda Mista Gabriel Aduda, tsohon ma'aikaci a hukumar EFCC wanda kuma kani ne ga Senata Philip Aduda ya samu mukamin direkta duk da cewa ya fadi jarrabawa na dole da doka ya tanada wa ma'aikatun gwamnatin tarayya kafin basu wannan matsayin.

Yin hakan ya ja cece-kuce a wannan lokacin amma gwamnatin tsohon shugaba Jonathan da ake zargi da asasa cin hanci da rashawa bata dau wani mataki a kai ba.

DUBA WANNAN: Yerima uku na Saudiyya sun bace daga Turai

Bayan shekaru 3 da faruwan haka, gwamnatin shugaba Buhari ta nada shi a matsayin babban sakatare, mukadashin shugaban kasa Yemi Osibanjo ne ya rantsar da shi tare da wasu mutane guda 14.

Manema labarai sunyi kokarin ji ta bakin mai magana da yawun mukadashin shugaban kasan Osibanjo, Laolu Akande, amma hakan yaci tura.

Amma wani ma'aikaci a ofishin Mista Osibanjo wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shine mai magana da yawun Mista Osibanjo din ba yace mukadashin shugaban kasan bai da bayani akan jarabawar Mista Gabriel Aduda. "Na tabbata Mista Osibanjo zai yi mamakin jin wannan batun" inji shi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel