Cin hanci da rashawa ya hana yan Najeriya cin moriyar Dimokradiyya - Osinbajo

Cin hanci da rashawa ya hana yan Najeriya cin moriyar Dimokradiyya - Osinbajo

-Osinbajo ya rantsar da sekatarorin gwamnatin tarayya guda 16

-Cin hanci da rashawa yayi wa Najeriya katutu

-Babu kasar da za ta iya aiwatar da manufofinta matukar akwai cin hanci da rashawa

Mukkadashin shugaban kasa, farfesa Yemi Osinbajo yace ba zai yiwu gwamnati ta iya aiwatar da manufofin ta a Najeriya ba, saboda yadda cin hanci da rashawa yayi katutu a kasar.

A jawabin shi yace babu kasar da za ta iya rayuwa da irin cin hanci da rashawa da Najeriya ke fuskanta, kuma idan haka yaci gaba zai hana yan kasan cin moriyar dimokradiyya.

Cin hanci da rashawa ya hana yan Najeriya cin moriyar Dimokradiyya-Osinbajo

Cin hanci da rashawa ya hana yan Najeriya cin moriyar Dimokradiyya-Osinbajo

Ya fadi hakane a lokacin da yake rantsar da sababbin seketarori gwamnatin tarayya na dindin-din a Abuja, da kuma ba wa ministocin da ya rantsar kwanakin baya ofisoshi.

KU KARANTA:Charly Boy,da kungiyarsa sun fasa zuwa Aso Rock yin zanga-zanga saboda tsoron rikici da ƙungiyar masu goyon bayan Buhari

“Ba ma tunanin akwai kasar da zata rayuwa idan ta fuskanci irin cin hanci da rashawa da kasar mu ta tsinci kanta aciki a shekarun baya. Ba zai taba yiwuwa gwamnati ta iya aiwatar da manufofin da talaka zai ci moriyar mulki dimokradiyya ba matukar ba a kawar da cin hanci da rashawa.

“Wannan sabon hakkin ne da ya rataya a wuyanku mussaman ku sababbin seketarorin da aka zabe ku bisa cancanta, da ku tabbtar da kawar da cin hanci da rashawa a wuraren ayyukan ku."

“Muna kyautata zatun zaku taimaki gwamanti wajen aiwatar da kudurorin da zai amfani talakawa,” Inji shi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel