Amurka da Koriya: Dan lukutin Korea ya fasa kaiwa dan lukutin Amurka harin dan lukutin bam na Nukiliya

Amurka da Koriya: Dan lukutin Korea ya fasa kaiwa dan lukutin Amurka harin dan lukutin bam na Nukiliya

Shekaru kusan saba'in kenan tun da Amurka ta kai hari kasar Koriya, inda a karshen yakin kasar ta rabe biyu, Koriya ta Kudu, mai bin irin tsarin Amurka na Jari Hujja wato Capitalism, da Koriya ta Arewa mai bin tsari irin na kasar Chana, wato Communism. Yanzu dai kowa yazo wuya.

Tun bayan hawansa kan karagar mulki a 2011, bayan rasuwar mahaiffnsa, dan wadan Koriya ta Arewa, Kim Jong-Un ya tsone ma Amurka ido, domin yaro ne dan shekaru 29 a lokacinmai zafin ra'ayi, mai taurin kai, wanda ke da sojoji miliyan biyu karkashin ikonsa.

Amurka da Koriya: Dan lukutin Korea ya fasa kaiwa dan lukutin Amurka harin Nukiliya
Amurka da Koriya: Dan lukutin Korea ya fasa kaiwa dan lukutin Amurka harin Nukiliya

Kim Il-Sung, Kakan wannan yaro dan shekara 35 shine ya kafa kasar Koriya ta arewa, kuma ya kulla kawancen kasarsa da kasashen Chana da ta U.S.S.R ta waccan lokacin, bayan rasuwarsa kuma ya bar wa Kim Jong-Il, uban na yanzu mulki, wanda shi kuma ya rasu a 2011 da ciwon zuciya.

Da hawan wannan yaro, sai ya kara kaimi wajen iyar da nufin kakansa na ganin kasarsu mai fama da talauci saboda gazawar tsarin nasu na gurguzu, da ma kuma takunkumai da majalisar manyan duniya ta kakaba wa kasar saboda kin bin dokokin ta.

Amurka da Koriya: Dan lukutin Korea ya fasa kaiwa dan lukutin Amurka harin Nukiliya
Amurka da Koriya: Dan lukutin Korea ya fasa kaiwa dan lukutin Amurka harin Nukiliya

Kafin a ankare, sai kawai aka ga kasar Koriya ta iya hada makami mai linzami mai cin dogon zango, wanda ka iya kaiwa kasashe masu nisa ciki harda Amurka, cikin rabin sa'a, kamar dai minti 30 kenan.

A dadai wannan lokaci kuma, suka sami damar hada bam na nukiliya mai kare dangi, suka kuma gwada karinsa a karkashin kasa, karfinsa kuma, ya razana kasashen yammacin duniya. Saukar Barack Obama ke da wuya, sai Donald Trump ya hau karadi da zagin Kim Jong-Un.

DUBA WANNAN: Sun Tsokalo Tsuliyar Dodo sun kashe soja a Nasarawa

A yanzu dai, an gano shi saurayi shugaban Koriya yana zaune da manyan janar Janar dinshi, da hotunan biranen Amurka a gabansa, da zanen yadda zasu kai musu hari a cikin makon nan, musamman tsibirin Guam, mai mutane kusan 200,000.

Wannan yasa Donal Trump bada umarnin a kakkabo duk wani makami mai linzami daga Koriyar, ya kuma sha alwashin kasa-kasa da Koriyar muddin ta gwada kai wa kasarsa hari.

Alamu dai na nuna shi Kim Jong-Un din ya saduda, inda ya ce ya dakatar da shirin sai yaga yadda 'rashin kunyar Yankees ta ci gaba', sannan zai dauki mataki a kansu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel