Hali zanen Dutse: Karanta abin da aka kama wani korarren jami’in DSS yana yi

Hali zanen Dutse: Karanta abin da aka kama wani korarren jami’in DSS yana yi

Hukumar Yansandan jihar Enugu ta sanar da kama wani tsohon jami’in rundunar tsaro ta sirri, DSS, wanda aka salla a kwanakin baya da laifin mallakar buhunan tabar wiwi guda 16.

Kaakakin rundunar, Ebere Amaraizu ne ya bada wannan sanarwa a garin Enugu inda yace sun samu nasarar kama wannan mutumi ne a ranar Litinin 14 ga watan Agusta bayan samun wasu rahotannin sirrri akansa.

KU KARANTA:

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito Kaakakin ya bayyana sunayen wadanda aka kama da suka hada da Emmanuel Ogbonna wanda aka gan shi da shaidar aiki na hukumar DSS mai dauke da sunan Emannuel Tanko, sai kuma abokin aikinsa Odo Chinedu.

Hali zanen Dutse: Karanta abin da aka kama wani korarren jami’in DSS yana yi
Ofishin Yansanda

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an gano buhunnan wiwin ne a cikin sashin ajiye kaya na motar su, wata kirar Camry mai lamba LSR 769 DF, kuma tuni an kama motar da wiwin.

Hali zanen Dutse: Karanta abin da aka kama wani korarren jami’in DSS yana yi
Korarren jami’in DSS

Sai dai Kaakakin yace bayan gudanar da bincike, sun gano cewar an sallami Ogbonna Emmanuel daga aikin DSS ne a shekarun baya, amma sai yake amfani da shaidar sa na aikin yana safarar wiwi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Me dame dame ya dace a gyara a Najeriya?

Asali: Legit.ng

Online view pixel