Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da ziyarar tawagar masu magana da yawun Buhari a Landan

Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da ziyarar tawagar masu magana da yawun Buhari a Landan

- Wasu ‘yan Najeriya sun fadi ra’ayoyinsu game da bidiyo da hotunan shugaba Buhari da tawagar masu magana da yawunsa

- A cikin bidiyon shugaba Buhari ya ce yana jin zai iya koma gida yanzu

- Shugaban ya ce yanzu ya fahimci bin umurnin, maimakon yin biyayya

'Yan Najeriya sun mayar da martani ga sanarwa da kuma bidiyon da aka gabatar a shafin yanar gizon bayan ziyarar tawagar masu magana da yawun shugaban kasar Muhammadu Buhari a Abuja House da ke birnin London.

A cikin bidiyon shugaba buhari ya ce: "Ina jin zan iya koma gida, amma likitoci suna kulawa . Yanzu na fahimci bin umurnin, maimakon a yi biyayya”.

A sakamakon haka, 'yan Nijeriya a kan dandalin watsa labarun zamantakewa ta Twitter sun ba da shawarwari ga shugaban.

Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da ziyarar tawagar masu magana da yawun Buhari a Landan

Shugaban kasar Muhammadu Buhari da tawagar masu magana da yawunsa a Abuja House da ke birnin Landan

NAIJ.com ta tattaro cewa, duk da yake wasu sun dage cewa Buhari ya yi murabus saboda a matsayinsa na shugaban kasa ya kamata ya saurare ‘yan Najeriya ba likitoci ba, wasu kuma sun goyi bayansa cewa ya ci gaba da zama har zai likitocin sun amince ya dawo.

KU KARANTA: Abinda mukayi a Gambia ya kankaro mana girma – Buhari

Ga wasu daga cikin ra’ayoyin ‘yan Najeriya:

@its_drjarfy : “Ya kamata ya koyi yadda zai saurari 'yan Nijeriya ta hanyar yin murabus".

@nature_222: “Shin, abin da 'yan Nijeriya suka zaba ke nan, ba ka jin kunyar ka ce irin wannan abu, duniya tana dariya yanzu haka”.

@ezediudum: “Abin sha'awa, likitocin Birtaniya ke ba shugaban kasar mu umurni”.

Duk da haka, wasu suna godiya ga sake dawo da shugaban kasa.

@Solabamigboye: “Godiya ga Allah saboda shugaba Buhari, amma idan mutane ba su tambaya ba, ba za ku nuna bidiyin a shafin yanar gizon ba. Harkokin adawa na da kyau ga dimokuradiyya”.

@AdemolaAdigun14: "Ina murnan ganin wannan bidiyo, ina kuma farin cikin ganin shugaban kasa a cikin isashen lafiya. Mutane masu hasada suyi tunani”.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel