'Yan Boko Haram sun kai hari a wani kauye sun kashe mutane

'Yan Boko Haram sun kai hari a wani kauye sun kashe mutane

- 'Yan Boko Haram na cigaba da kai hari a Maiduguri

- Dazu mu ji cewa an kashe wasu mutane 4 a wani hari

- Har wa yau kuma da dama sun samu rauni a harin

Mun samu labari cewa 'Yan ta'addan Boko Haram na cigaba da kai hari a wasu Kauyukan da ke cikin Jihar Borno.

'Yan Boko Haram sun kai hari a wani kauye sun kashe mutane

'Yan Boko Haram sun kai hari

Dazu muka ji cewa an kai wani hari a wani Kauye da ake kira Amarwa da ke kan hanyar zuwa Garin Maiduguri kamar yadda Jaridar Daily Post ta bayyana. An rasa mutane 4 a harin inda wasu kuma suka samu rauni.

KU KARANTA: Za a kata tsaro wajen ibada-Minista

Wata majiya da ke kusa da inda wannan abu ya faru a Garin Konduga ta ga traffic da wannan. Bayan nan ma an kona wani Kauye da ake kira Wanori a Daren jiya. Yanzu haka dai an yi asibiti da wasu yayin da Jami'an tsaro ba su ce komai ba.

Kwanan nan dai Shugaban Hafsun Sojin kasar Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai ya fadawa Rundunar Sojojin Najeriya a shiga duk wani kwararo da sako a kama 'Yan ta'addan Boko Haram a duk inda su ka buya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An kama masu satar Jama'a

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel