Zaman Buhari a Ingila: Ahmed Joda yayi kira ga Majalisa da ta zartas da hukuncin tsarin mulki

Zaman Buhari a Ingila: Ahmed Joda yayi kira ga Majalisa da ta zartas da hukuncin tsarin mulki

Hira da Ahmed Joda, dattijon Arewa, kuma tsohon jakadan Najeriya, kuma makusanci ga shugaba Buhari, ya zayyana yadda ya kamata shugaba Buhari yayi, ko kuma majalisa su san yadda zasu yi dashi, kamar yadda wai tsarin mulki ya tanada

Mutumin da ya shugabanci tawagar Shugaba buhari domin karbar Mulki daga hannun tsohon shugaba Jonathan bayan kammala zaben 2015, Ahmed Joda ya yi kira ga majalisun Nigeria da su zartar da abin da kundun tsarin mulki ya fada idan shugaba ya wuce kwanaki 90 baya kasa. A doguwar tattaunawa da yayi da yan jaridu joda, ya ce Nigeria tana da kundun tsarin mulki da ya fayyace duk yadda za a tunkari ko warware kowace irin takardama.

Zaman Buhari a Ingila: Ahmed Joda yayi kira ga Majalisa da ta zartas da hukuncin tsarin mulki

Zaman Buhari a Ingila: Ahmed Joda yayi kira ga Majalisa da ta zartas da hukuncin tsarin mulki

A saboda haka ne da a ka tambaye shi ra'ayinsa kan zaman jinyar Shugaba Buhari a birnin London wanda yanzu haka ya shafe sama da kwana ki 90 da kundin Nigeria ya kunsa, sai ya ce a duba kundin Nigeria a kuma zartar da duk abinda ya fada a kan shugaba Buhari.

Dattijo, joda, ya yi tsokaci a kan batutuwa da dama da ke faruwa a kasa da irin gwagwarmayar aiki da kalubale da ya fuskanta.

Daga karshe ya nuna takaicin sa ga wutar kabilanci da kalamai masu haddasa tsana tsakanin kabilun Nigeria ke ruruwa. Ya yi kyari ga yan Nigeria da su guji duk wani abu da Ka iya tsoma kasar cikin rikicin kabilanci kamar yadda ta taba faruwa shekaru da dama suka wuce. Joda, ya ce yan Nigeria su zama tsintsiya madaurin ki daya.

DUBA WANNAN: Sanata Akpabiyo yace su PDP basu goyon bayan rarrabuwar Najeriya

Shugaba Buhari dai yayi mursisi da masu kiran yayi murabus ko ya dawo, yace sai likitoci sun sallame shi tukun, badine kuma jam'iyyarsa zata fitar da dan takarar shugaba a 2019.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel